Rundunar sojin saman Najeriya ta ce tana gudanar da bincike kan zargin cewa sojojinta sun kashe sojojin kasa 20 a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.
Wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Litinin ta ce an ja hankalinta kan rahotannin da ke nuna cewa sojinta sun kashe sojn kasa a wani farmaki ta sama a garin Mainoko da ke da nisan kilomita 55 daga Maiduguri.
"Rundunar sojin sama tana son ta bayyana cewa tana gudanar da bincike kan hotuna da bidiyon da ake watsawa a yanzu kuma za ta sanar da jama'a a game da zargi kan wannan lamari," in ji sanarwar.
investigated and the general public will be duly updated on the alleged incident. All inquiries should please be directed to the Office of the Director of Public Relations and Information, Headquarters Nigerian Air Force or forwarded to info@airforce.mil.ng.
— Nigerian Air Force (@NigAirForce) April 26, 2021
- 2/2
Hakan na faruwa ne a yayin da rahotanni ke nuna cewa an kashe sojoji da dama yayin harin da mayakan kungiyar IS da ke Yammacin Afirka suka kai kai kan sansaninsu da ke jihar ta Borno.
Kodayake hukumomi ba su bayyana adadin sojojin da aka kashe ba, amma wasu majiyoyin tsaro sun shaida wa BBC cewa kusan sojoji 30 aka kashe yayin harin.
Majoyoyinmu sun kara da cewa mayakan kungiyar ta IS da ke Yammacin Afirka dauke da muggana makamai cikin motocin yaki kusan 12 ne suka kai hari kan sansanin sojin da ke Mainok ranar Lahadi, inda suka bude musu wuta.
Bayanai sun nuna cewa rundunar sojin saman Najeriya ta mayar da martani ta hanyar yin luguden wuta domin taimaka wa sojin kasa.
Sai dai majiyoyinmu sun ce an kashe sojoji fiye da talatin - wasu daga cikinsu bisa kuskure.
Hakan ne ya sa rundunar sojin saman ta ce tana gudanar da bincike kan lamarin.
Kazalika mayakan Boko Haram sun kai hari a garin Geidam na jihar Yobe mai makwabtaka da jihar Borno inda suka saje a ckin jama'a.
Mutanen da dama da ke ci gaba da tserewa daga garin sun shaida wa BBC mayakan Boko Haram sun kashe fararen hula da dama ciki har da wani malamin makarantar firamare wanda ska datse kansa.
Amma mai magana da yawun rundunar sojin kasa Birgediya Janar Mohammed Yarima ya shaida wa BBC cewa sojoji sun kashe mayakan Boko Haram 21.