Menu

Buhari ya bai wa ƴan bindigar Zamfara wa'adin wata biyu su miƙa wuya

 117514873 Buharifushigetty Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya

Wed, 10 Mar 2021 Source: BBC

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya bai wa ƴan bindigar da ke jihar Zamfara a arewacin Najeriya wa'adin wata biyu su miƙa wuya.

Gwamnan jihar Bello Matawalle ne ya faɗi hakan a wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin a ranar Talata da daddare.

Gwamna Matawalle ya kuma ce shugaban ƙasar ya bayar da umarnin kai ƙarin dakarun tsaro 6,000 jihar don murƙushe ƴan bindigar idan har suka ƙi miƙa wuya.

Jawabin gwamnan na zuwa ne a daidai lokacin da hare-haren ƴan fashi a ƙauyuka da kuma satar mutane ke ƙaruwa a jihar.

Gwamna Matwalle ya ce Shugaba Buhari ya yi wannan alƙawari ne a lokacin da ya kai wata ziyarar aiki Abuja don gana wa da shugaban da sauran manyan masu ruwa da tsaki kan sha'anin tsaro, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ambato.

"A tattaunawar da na yi da Shugaba Muhammadu Buhari da wasu manyan masu ruwa da tsaki a Abuja, an yanke shawarar cewa za a kawo ƙarin dakarun tsaro 6,000 don su haɗa hannu da waɗanda ke ƙasa wajen daƙile matsalolin tsaron jihar.

"Nan ba da daɗewa ba dakarun za su iso jihar don fara ayyukansu, kuma muna godiya ga gwamnatin tarayya.

"Sannan kuma shugaban ƙasa ya amince da ƙayyade lokacin da ya kamata ƴan bindigar su miƙa makamansu su kuma shiga cikin shirin sasantawar da ake yi," a cewar gwamnan.

Gwamna Matawalle tun bayan hawansa mulki ya ƙaddamar da shirin sasantawa da ƴan bindigar, abin da gwamnatin jihar take ganin yana aiki.

"Yarjejeniyar sasantawa da gwamnatina ta yi nasara wajen kuɓutar da ɗaruruwan mutanen da aka sace da buɗe kasuwanci da dawo da harkokin kasuwanci a faɗin jihar.

Sai dai gwamnan ya ce duk da cewa an dan samu zaman lafiya sakamakon sasantawar, wasu ƴan bindigar har yanzu sun ƙi shiga cikin shirin suna ci gaba da kai hare-hare kan wasu al'ummomin.

"Kuma gwamnati ta gano masu yi mata ƙafar ungulu a ciki da wajen jihar kan harkar tsaro," in ji Matawalle.

Akwai ƴan bindiga 30,000 a jihar Zamfara

Jawabin gwamnan na zuwa ne sa'o'i kaɗan bayan da sarakunan gargajiya na jihar suka ce akwai fiye da ƴan bindiga 30,000 a fadin jihar Zamfara.

Sarakunan sun gaya wa hafsoshin tsaron ƙasar wannan magana ne a yayin da suka kai ziyarar aiki jihar.

Sun ƙara da cewa yawan ƴan bindigar ya fi na jami'an tsaro 10,000 da a yanzu haka ke jihar don yaƙi da masu kai hare-haren.

Gwamnan ya bai wa sarakunan gargajiyan da shugabannin ƙananan hukumomi umarnin sa ido kan shige da ficen duk wani da ba a gamsu da shi ba.

Kazalika ya haramta ɗaukar fiye da mutum biyu a kan babur. "Babu zirga-zirgar babura a duk lungu da saƙon jihar kuma an bai wa jami'an tsaro umarnin kama duk wanda ya karya doka," a cewarsa.

Sabbin matakan tsaro da gwamna ya sanar

Sarakunan gargajiya da shugabannin ƙananan hukumomi su dinga zama a garuruwansu An haramta amfani da babura da yawa a lokaci ɗaya

Za a hukunta duk wanda aka kama da yada labaran karya a kafafen sada zumunta

Za a hukunta duk dan siyasar da aka kama da haddasa rikici da ɓata lamarin tsaro

An hana mutum biyu hawa babur ɗaya

Matawalle ya kuma jaddada haramta ayyukan ƴan sa kai a jihar, inda ya ce za a hukunta duk wanda aka kama da bindiga.

Source: BBC