Za a bar 'yan kallo 8,000 su shiga kallon wasan karshe na kofin Carabao da za a buga tsakanin Tottenham da Manchester City.
Wannan ne gwajin farko da za a yi na barin 'yan kallo masu yawa tun bayan dakatar da shiga filayen wasa a Ingila.
Za a raba tikitin shiga wasan tsakanin magoya bayan kungiyoyin biyu a wasan da za a buga a filin kwallo na Wembley a ranar 25 ga watan Afrilu.
Za kuma a sayarwa da sauaran masu kallo abin da ya yi saura na tikitin.
Ricky Parry, shi ke jagorantar hukumar shirya lig ta Ingila ya ce wannan wata gagarumar nasara ce.
A ranar 18 ga watan Afrilu, za a bar 'yan kallo 4,000 su shiga wasan daf da nakarshe da za a buga tsakanin Leicester City da Southampton.
A ranar 15 ga watan Mayu kuma da za a buga wasan karshe za a bar mutum 21,000 su shiga kallo.
A wasannin ne tsa a fara gwada shaidar karbar rigakafin korona, ga wanda duk sakamakon ya nuna ba shi da cutar to zai shiga filin wasa.