Ranar Talata Chelsea za ta buga wasa na biyu da FC Porto a zagayen quarter finals da za su kece raini a Sevilla ta Spaniya.
A wasan farko da suka buga ranar Laraba, Chelsea ce ta yi nasara da ci 2-0 a matakin ita ce bakuwa, kuma Mason Mount da Ben Chilwell ne sukla ci mata kwallayen.
Tuni dai Thomas Tuchel ya fayyace 'yan wasan Chelsea 23 da za su fuskanci Porto a karawar da za su yi a Sevilla zagaye na biyu a matakin gidan kungiyar Stamford Bridge.
Cikin 'yan kwallon Chelsea har da Andreas Christensen wanda bai buga gasar Premier ba a karshen mako da ta doke Crystal Palace ba.
Haka kuma Chelsea wadda a safiyar Litinin ta je Spaniya har da Thiago Silva cikin 'yan kwallon da ake sa ran zai buga fafatawar ranar Talata.
Thomas Tuchel ya ja ragamar Chelsea wasa 17 tun daga Janairu a dukkan fafatawa, ya ci wasa 12 da canjaras hudu yi rashin nasara a wasa daya.
Jerin 'yan wasan Chelsea 23 da za su kara da Porto: