China ta kara watsi da shirin sanya wa shugabannin soji na Myanmar takunkumi, a wani taron gaggawa na kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.
Jakadanta a majalisar ya ce daukar wannan mataki a kan sojojin ba abin da zai haifar illa kara tabarbarewar al'amura a kasar.
Tun bayan da sojin suka yi juyin mulki, a ranar daya ga watan da ya gabata na Fabrairu ake ta yin bore na kin amincewa mulkin nasu.
Tsayin dakan da China ta sake yi na ganin kwamitin tsaron bai kakaba wa sojojin na Myanmar takunkumin ba, ya biyo bayan kiran da wakiliya ta musamman ta majalisar dinkin duniyar Christine Schraner Burgener, ta yi ne inda ta bukaci kwamitin da ya dauki mataki a kan sojojin.
Ta yi gargadin kan yadda take ganin al'amura za su iya kara cabewa, a rikicin kasar, ta yadda zai iya kaiwa ga asarar dimbin rayuka, da kuma yakin basasa, kan yadda sojojin ke mayar da martini kan boren da ake musu na kin yarda da juyin mulkin.
Masu raji sun ce tuni daman sojojin sun hallaka mutane sama da dari biyar a cikin wata biyu na bayan juyin mulkin.
Birtaniya ce dai ta kira taron gaggawar na kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniyar a wannan karon, bayan kashe sama da masu zanga-zanga dari daya, a rana daya, a karshen makon da ya gabata.
Da take magana kafin taron jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield, ta sake yin kakkausar suka kan cin zalin da ake yi a Myanmar a baya bayan nan.
Ta ce; ''Abin da sojin suke yi a Burma ga al'ummar Burma, tashin hankalin, hare-hare, kisan yara, abu ne mai tayar da hanakli, da kuma ba za a amince da shi ba.
Saboda haka ba za mu koma baya mu tsaya kawai muna ganin hakan na ci gaba da faruwa ba. Dole ne mu ci gaba da matsawa.''
Kungiyar agaji da kare hakkin dan adam ta Save the Children a wani rahoto da ta fitar ta ce sojojin na Myanmar sun kashe yara akalla 43 tun lokacin da suka yi juyin mulkin a ranar daya ga watan na Fabrairu.
Wata kungiya da ke kasar wadda ke bin diddigin abubuwan da ke faruwa ta fitar da alkaluman jumullar mutanen da ta ce ta tabbatar sojin sun kashe, 521.
Matsayin China na bayar da kariya ga Myanmar abu ne da daman tun kafin juyin mulkin na yanzu take yi, tare da Rasha, don gainin Majalisar Dinkin Duniyar ba ta soke ta ba ballanatana har ta kai ga sanya wa kasar takunkumi tun ma a kan yadda take yi wa Musulmi 'yan Rohingya.
Hakan ko ana ganin ba ya rasa nasaba da yadda gwamnatin Chinar ke kallon Myanmar mai muhimmanci gare ta ta fannin tattalin arziki, baya ga kasancewarta daya daga cikin kawaye na kut da kut.