Menu

'Cin zarafin mace na cire mata yarda da amana'

 117511240  113747111 Mediaitem113747109 'Cin zarafin mace na cire mata yarda da amana'

Wed, 10 Mar 2021 Source: BBC

Wani sabon rahoto na Hukumar Lafiya ta Duniya ya gano cewa kashi ɗaya bisa uku na matan duniya na fuskantar cin zarafi a wani mataki na rayuwarsu.

Rahoton shi ne mafi girma da aka taɓa yi kan cin zarafin mata, kuma an tattaro wasu bayanan ne tun daga abubuwan da suka faru daga shekarar 2000 zuwa 2018.

Rahoton kuma ya ce akwai yiwuwar tasirin annobar korona zai ƙara yawan wannan cin zarafin.

Rahoton kuma ya ce cin zarafin abokan zama ya fi yawaita, inda ya shafi sama da mata miliyan dari shida da arba'in a duniya.

Kashi ɗaya cikin huɗu na matan da ke tsakanin shekara 15 zuwa 24 sun riga sun fuskanci cin zarafin daga abokan zamansu, a cewar rahoton.

Matsalar ta fi ƙamari a yankin kudancin Asiya da kasashen kudu da Saharar Afirka da Oceania.

Dr. Mairo Mandara, mai fafutukar tabbatar da 'yancin mata a Nijeriya ta shaida wa BBC cewa rahoton ba abin mamaki bane saboda "a matsayina na likita, na san da yawa na kan ga mata da suke cikin uƙuba waɗansunsu ma a cikin (rayuwar) aure".

Ta ce batun cin zarafin mata abu ne da ya zama ruwan dare - babu yare, babu addini, babu masu kuɗi babu talaka "gwara ma a ce maganar ilimi, ilimi ne kawai ya banbanta a wannan harkar".

A cewarta, mata sun fi fuskantar wulaƙanci - "mata da mijinta sun zauna shekara 30, amma ba ta fi ƙarfin wulaƙanci ba".

Ta bayyana yadda a lokacin kullen korona aka riƙa samun ƙaruwar cin zarafin mata a gidajen aure - "fyaɗe ga yara ƙanana ya ƙaru, mata da ke zaune da mazajensu shekara da shekaru ba su taɓa sanin mazansu na duka ba, suka fara duka, rigingimu kala-kala suka fito".

Illar cin zarafi ga mata

Dr Mairo Mandara ta ce cin zarafi na da babbar illa ga mata duk da a cewarta matan suna haƙuri amma "zai cire yarda da amana".

Ta ce abin da mutane ba su gane ba shi ne "duk wulaƙancin da ake yi wa mata mai ƴaƴa, ƴaƴn suna gani, ko ita ta manta, ƴaƴan ba sa mantawa, za ki ga idan ƴaƴa maza ne da suka ga iyayensu maza suna wulaƙanta iyayensu mata, suma za su tashi suna wulaƙanta mata".

Mafita ga matsalar cin zarafin mata

A cewar mai fafutukar tabbatar da ƴancin matan, mafitar wannan matsala ita ce tsoron Allah - imanin sanin cewa duk abin da mutum ya yi Allah zai tambaye sa.

"Sanin cewa mace mutum ce kamar kowane mutum kuma duk wanda ya wulaƙanta wata mace, ya sani cewa mahaifiyarsa mace ce, yarsa mace ce, ƴarsa mace ce, matarsa mace ce, macen nan da dai ake gani ita ce dai uwa" kamar yadda Dr Mairo Mandara ta faɗa.

Source: BBC