Menu

DMX, Mawaki kuma tauraron fina-finan Amurka ya mutu yana da shekara 50

 117942853 Gettyimages 1173545968 Mawaki kuma tauraron fina-finan Amurka DMX

Sat, 10 Apr 2021 Source: BBC

Mawaki kuma tauraron fina-finan Amurka DMX ya mutu yana da shekara 50, kwana biyar bayan ya yi fama da bugun zuciya.

An sanya mawakin, wanda sunansa na ainihi shi ne Earl Simmons, ya jikin na'urar da ke taimaka masa yin numfashi amma ya mutu a kusa da iyalinsa da ke jinyarsa.

A cikin wata sanarwa, iyalansa sun ce mawakin ya "kasance gwarzo wanda ya yi fafutuka har karshen rayuwarsa".

"Wakokin Earl sun ja hankalin mutane da dama a fadin duniya kuma ba za a taba mantawa da gudunmawar da ya bayar ba."

DMX, wanda ake kira Dark Man X, yana cikin manyan mawaka salon hip-hop wanda ya hada gwiwa da mawaka irin su JAY-Z, Ja Rule da LL Cool J.

Fitattun wakokin da ya yi sun hada da Party Up (Up in Here) da X Gon' Give It To Ya.

Kazalika ya fito a fina-finai da dama kamar su Cradle 2 the Grave, Romeo Must Die da Exit Wounds.

An haife shi a Mount Vernon, da ke New York a 1970, kuma DMX ya gamu da jarabar shan miyagun kwayoyi shekaru da dama inda aka kai shi gidan kula da masu shan miyagun kwayoyi.

Mawakin mai 'ya'ya 15 ya yi zaman gidan yari saboda samunsa da laifuka da dama wadanda suka hada da cin zarafin dabbobi, tukin ganganci, mallakar miyagun kwayoyi da makamai.

A cewar iyalinsa, DMX ya mutu ranar Juma'a a asibitin White Plains da ke White Plains, New York.


Source: BBC