An dage gudanar da babban taron jam'iyyar adawa a Najeriya PDP na shiyyar arewa maso yammacin kasar da ya kamata ya gudana a jihar Kaduna.
Dage wannan taro na zuwa ne bayan wani yamutsi da ya barke dai dai lokacin da aka soma kada kuri'a.
Wannan yankin na arewa maso yamma dai ya kunshi jihohi 7 da suka hada da Jigawa da Kano da Kaduna da Katsina da Kebbi da Sokoto da Zamfara.
Aliyu Bello Mai Kusa, shi ne shugaban matasan jam'iyyar ta PDP a jahar Kaduna ya bayyana wa BBC cewa abin da ya faru a jihar Kadunan alamun nasara ne ga PDP a zaben 2023.
"Duk abin da akwai nasara a ciki duk abin da yake da kyau dole ne sai an yi jayayya, wannan yana nuna cewa a shekarar 2023, jam'iyyar PDP za ta kori jam'iyyar APC a mulki, a zo a yi tsarin da talakawa za su samu walwala a samu tsaro da ci gaba mai dorewa da samar wa matasa aiki a Najeriya". in ji Aliyu Bello Mai Kusa.
A cewarsa, an fara tantance wadanda za su kada kuri'a, inda jihar Kebbi da jihar Sokoto suka fara kada kuri'a - "magoya bayan wani dan takara suna ganin dan takararsu ba zai samu nasara ba sai suka ta da hatsaniya suka fasa akwatin zabe kuma suka yaga takardun da za a kada kuri'a".
Ya ce wannan dalili ne ya sa manyan jam'iyyar suka dauki matakin dage zaben.
Shugaban matasan jam'iyyar ta PDP ya ce a shirye suke su amince da yin biyayya ga duk wani mataki da manyan jam'iyyar za su dauka domin a ceto yan Najeriya daga halin da suke ciki.
Tun da farko dai daya daga cikin iyayen jam'iyyar a yankin Sanata Rabiu Kwankwaso ya zargi gwamnan jihar Sokoto Gwamna Aminu Waziri Tambuwal da yin katsalandan cikin al'amuran jam'iyyar a jihar Kano.
A cewar Kwankwaso wanda yake jagorantar bangaren Kwankwasiyya ya zargi Tambuwal da hada kai da wasu ƴaƴan jam'iyyar na Kano da ke hamayya da shi da mutanensa don taimaka musu su samu shugabancin jam'iyyar na yankin Arewa maso Yamma.
To sai dai a nasa bangaren, gwamna Aminu Tambuwal ya musanta wannan zargin inda ya ce "duk wanda yake da sha'awa ya fito ya yi takara."