Gwamnatin Jihar Neja da ke arewacin Najeriya ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun gwamnati da ke jihar tsawon mako biyu.
An cimma wannan matsaya ne bayan wata tattaunawa tsakanin gwamnati da jami'an tsaro na jihar kuma za a rufe su ne daga Juma'a 12 ga watan Maris zuwa 26 ga watan na Maris.
Tun farko ma'aikatar ilimi a jihar ta yi wata ganawar gaggawa da shugabannin ƙungiyar masu makarantu masu zaman kansu da sauran masu ruwa da tsaki a jihar.
A jihar Neja, kusan mutum 100 'yan bindiga suka saki a watan Fabarairu, ciki har da ɗalibai 27 bayan sun shafe kwanaki suna garkuwa da su.
"Mun yanke shawarar rufe makarantun ne na tsawon sati biyu domin jiran jami'an tsaron nan su zo mana da bayanan tsaro na dukkan makarantun," in ji ta.
Ta ƙara da cewa "muna so ne mu tabbatar cewa ɗalibai sun yi karatu cikin tsaro a kowace makaranta".
Game da kai jami'an tsaro ƙofar makarantun domin bayar da tsaro, kwamishiniyar ta ce ya zuwa yanzu suna da tsare-tsare na nan take da kuma na dogon zango.
"Daga cikin abubuwan da muke dubawa yanzu su ne, jami'an tsaro za su ba mu shawarwari tun da da ma ɓangarensu ne, ita kuma gwamnati za ta duba domin ganin abin da za ta yi.
"Cikin sati biyun nan za mu duba abubuwan da kuma tsare-tsaren da kowace makaranta za ta yi."
Hajiya Hannatu ta ce suna duba yiwuwar haɗe wasu makarantun kwana da kuma na je-ka-ka-dawo duka dai saboda dalilai na tsaro.
Ƴan sanda da sojoji duka suna ƙarƙashin ikon gwamnatin tarayya - kuma biyan kuɗin fansa, ya ƙara haifar satar mutane a matsayin wata babbar hanyar samun kuɗi.
Wannan zargi ne da gwamnonin suka musanta. Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, wanda a baya ya ba wa ƴan fashi" tubabbu" gidaje da kudi da motoci, ya ce mutane" ba su gamsu da shirin nasa na zaman lafiya ba "suna yin zagon kasa ga kokarinsa na kawo karshen rikicin.
Kafin yanzu, waɗanda aka fi yin garkuwa da su matafiya ne a yankin arewa maso yammacin Najeriya, waɗanda suka biya tsakanin dala 20 zuwa dala 200,000 domin tsira, amma tun sace ɗaliban makarantar Chibok 276 a 2014 da Boko Haram ta yi a jihar Borno, ƴan bindiga da dama sun bi tafarkin.