BBC

Actualités

Sport

Business

Culture

TV / Radio

Afrique

Opinions

Pays

MenuAfrique
BBC

Dalilin da ya sa shugaba Buhari ya kafa cibiyar yaƙi da ƙananan makamai a Najeriya

 118312615 B4b8ed4e 5022 4bca 843b 2819edc27449 Shugaba Muhammadu Buhari

Tue, 4 May 2021 Source: BBC

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da kafa cibiyar yaƙi da kananan makamai (NCCSALW) wadda za ta kasance karkashin ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro.

Ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara a kan harkokin tsaro ya ce cibiyar za ta maye gurbin kwamitin shugaban ƙasa kan kananan makamai da aka rusa.

Gwamnatin Najeriya ta ce matakin na cikin tsare-tsaren da ta bulo da su domin sauya fasalin tsaron ƙasar da zummar shawo kan barazanar da ake fuskanta daga ƙananan makamai da ake safararsu cikin ƙasar.

Ta kuma ce sabuwar cibiyar za ta karfafa cibiyoyi tsaro a kan yadda za su dinga sa ido a kan kananan makamai.

Ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara a kan tsaro ya ce ƙananan makamai da bindigogi da ake shigowa da su cikin ƙasar daga ƙasashen waje da kuma yankin sahel sun sa ana samun ƙaruwa a hare-haren 'yan ta'ada da masu fataucin mutane, da masu aikata miyagun laifuka da masu tada ƙayar baya a yammacin Afrika da Najeriya.

Cibiyar za ta kuma aiwatar da yarjejeniyar ECOWAS a kan ƙananan makamai da ake shigowa da su cikin yankin da wadanda ake fitarwa da kuma dokar mjalisar dinkin duniya da ta haramta sayar da ƙananan makamai ta haramtaciyyar hanya.

Source: BBC