Menu

'Dalilin da ya sa yan bindiga a Najeriya ba za su mika wuya ba' - Sheikh Gumi

 117697286 999462a6 B9de 4159 9755 3cc2db7d3c79 Sheikh Ahmed Gumi

Thu, 25 Mar 2021 Source: BBC

Babban malamin addinin musuluncin nan a Najeriya, Sheikh Ahmad Gumi ya ce watakila yan bindiga ba za su so su ajiye makamansu ba idan ba tabbacin tsaron lafiyarsu.

Malamin, wanda yake kokarin kawo karshen rashin tsaro ya nanata cewa tattaunawa ita ce mafita.

Babu wanda zai iya ba da hujjar aikata laifi, abin da mu ke cewa shi ne abin da muka gani a daji, fada ne na kabilanci da ke faruwa tsakanin muutane a cikin dajin da kauyukan da ke makwabtaka da su.

Lokacin da makiyayin ya ji yana da korafi kuma ba wanda ya saurare shi, sai ya dauki makami''.

Sheikh Gumi ya ce shi yasa yan bindigar suka tattauna da su lokacin da suka je dajin

Don haka lokacin da muka je can suka ga mai saurare, a shirye suke su tattauna, su gaya mana korafinsu, kuma a shirye suke su shigo cikin al'umma.

Don haka a irin wannan yanayi, ban ga dalilin da zai hana mu tattaunawa da su ba.

Malamin ya kuma ce yana da matukar hadari a kyale samarin da ba su da ilimi suna ta'amaali da kwayoyin da ke sa maye.

Source: BBC