Menu

Daunte Wright: Yadda sabuwar tarzoma ta ɓarke a Amurka kan kisan bakar fata 'bisa kuskure'

 118009687 Mediaitem118009686 Tarzoma ta barke kan harbe wani bakar fata da wata jami'ar 'yan sanda ta yi

Wed, 14 Apr 2021 Source: BBC

Mutane kimanin 40 ne aka cafke a arewacin birnin Minneapolis na Amurka a dare a biyu na tarzomar da ta barke kan harbe wani bakar fata da wata jami'ar 'yan sanda ta yi.

Masu zanga-zanga a Tsakiyar Brooklyn sun ki bin dokar hana fita inda suka rika jifan 'yan sanda su kuma suka rika mayar da martani da hayaki mai saka kwalla da gurneti marar hadari.

'Yan sanda sun ce an kashe Daunte Wright, mai shekaru 20, bayan da wata 'yar sanda ta harbe shi da bindigar da ta yi zaton na'urar kashe laka ce.

Harbin na faruwa ne bayan da ake ci gaba da sauraren karar kisan bakar fata George Floyd a kotun da ke da nisan mil kadan daga wurin da aka tuhumi tsohon dan sanda Derek Chauvin da kisan bakar fatar a cikin watan Mayun shekara da ta gabata.

A ranar Litinin ne lauyoyi masu kare Derek Chauvin suka bukaci a cire masu taimaka wa alkali - a raba su daga sauran mutane - don mai yiwuwa abin da ke faruwa zai iya yin tasiri a kansu.

Amma kuma alkalin bai amince da bukatar tasu ba.

An bayyana 'yar sandar da ta harbe Mista Wright da suna Kim Potter, mai shekaru 48, wadda ta yi aiki a helkwatar 'yan sanda ta Tsakiyar Brooklyn tsawon shekaru 26.

A ranar Lahadi ne aka fito da Mista Wright daga cikin mota aka tsayar da shi a kan karya dokar tuki, amma an samu sa-in-sa bayan da ya nemi ya koma cikin motarsa.

Bayan da ta fito da bindigarta a bisa kuskure, jami'ar 'yan sandan ta ce: "Kash, na harbe shi."

Me ya faru a cikin daren?

Ana ci gaba da aiwatar da dokar hana fita daga karfe bakwai na dare (tsakar dare agogon GMT).

A wani taron manema labarai bayan tsakar dare, babban jami'n 'yan sandan sintiri a jihar Minnesota, Kanal Matt Langer, ya ce jami'an sun kai ga masu shirya zanga-zangar domin kokarin kwantar da tarzomar amma "abin takaici yunkurin bai kai ga nasara ba, kana wadanda suka shirya sun kasa shawo kan masu zanga-zangar."

Kanar Langer ya ce an yi ta "jifan jami'an da tarkace" da suka hada da tartsasin wuta.

Ya ce masu zanga-zangar sun kai ga jikin katangar helkwatar 'yan sanda ta Tsakiyar Brooklyn kuma an yanke shawarar mayar da su baya.

An yi ta sace-sace da kwasar ganima a yankin da wasu yankunan Minneapolis da St Paul mai makwabtaka.

A martaninsa game da tarzomar, shugaban Amurka Joe Biden ya ce zanga-zangar "a bisa hanya take" amma ya kara da cewa: "'Ina so na tabbatar da cewa kuma: babu wani dalilin da zai sa a rika sace-sace."

Kafin tsakar daren, Magajin Garin Tsakiyar Brooklyn Mike Elliot ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: "Yanzu hankali ya kwanta a birninmu, mun gode muku duka da kuka fito zanga-zanga cikin lumana kana kuka koma gida."

Ya kuma ce ya yi magana da mahaifin Daunte Wright, kuma zai yi "duk abinda ya dace don tabbatar da an yi adalci".

Wakiliyar BBC Barbara Plett-Usher ta aiko da rahoto daga wurin

Wata alama a zanga-zangar ta dauke hankulan kowa: "Lokacin shari'ar!!?" an rubuta da haruffa masu launin ruwan goro.

"Ba daidai ba ne," in ji wani matashi dauke da shi."Sun san cewa suna da dangantaka mai tsami tsakaninsu da al'ummar bakaken fata a yanzu haka, kuma ya kamata a ce sun nemi yadda za su kawo gyara, ba wannan ba."

Mahukuntan birnin sun ce da bai kamata a ce an yi harbi a cikin wannan yanayi mai tsanani ba, da ake cikin damuwa game da batun kisan George Floyd.

Wasu masu zanga-zangar na jifa da kwalabe tare da jefa tartsatsin wuta a daidai wurin jami'an 'yan sandan. Sun nuna fushinsu yayin da jami'an suka ja daga. "Kun kashe shi, a wane dalili?" wata matashiya ta yi ihu.

"Ɗa ne, kuma uba ne, kuma bakar fata ne da ya kamata ya rayu."

"Kun san bambanci tsakanin bindiga da kuma na'urar harbi mai amfani da lantarki?" wani ya daka tsawa.

"Babu zancen kuskure a nan," in ji wani mutum. "Gaskiyar magana ita ce, mun rasa karin wani matashi bakar fata daga wata jami'ar 'yan sanda.

Me ya faru da Daunte Wright?

Shugaban 'yan sanda Tim Gannon ya yi cikakken bayanin matakin da 'yan sanda suka dauka bayan da aka fito da Mista Wright waje, yana cewa ya yi amanna harbin da aka yi a bisa "kuskure ne."

A lokacin taron manema labarai a ranar Litinin, ya saka wani gajeren faifen bidiyo daga na'urar daukar hoto da ke jikin jami'ar da ke nuna Mista Wright na kokarin komawa cikin motarsa yayin da jami'an ke kokarin saka masa ankwa a bakin hanya.

Ana iya jin wani jami'i na ambatar na'urar harbi yana cewa "Taser, Taser, Taser" - yadda tsarin 'yan sanda yake kafin ya harba daya daga cikin bindigogin robar.

Ana iya ganin Mista Wright yana shiga motarsa yana tafiya, yayin da kuma jami'ar ta bayyana amfani da irin waccan na'urar ta harbe shi.

Bayan da ya samu mummunan rauni, Mista Wright ya yi karo da motar a kan wani titi da ke kusa.

"Na yi ammana wannan jami'a tayi niyyar amfani da na'urar Taser ne amma ta harbe shi da harsashi daya," in ji shugaban 'yan sanda Gannon, ya kara cewa: "Babu wani abu da zan fada da zai rage kaifin bakin cikin."

An bai wa jami'ar hutun dole - na wucin gadi tare da biyan alawus da albashi.

Magajin Garin, Elliot ya ce kamata ya yi a sallame ta daga aiki. Zai yanke shawara a ranar Talata kan ko Gannon zai ci gaba da rike mukaminsa, kamar yadda jaridar StarTribune ta ruwaito.

Dalilin da ya sa Minneapolis ke cikin damuwa

Ana kan shari'ar Derek Chauvin kan kisan George Floyd a birnin har na tsawon makonni biyu a yanzu.

An dauki faifen bidiyon Mista Chauvin yana durkushe a kan wuyan Mista Floyd har na tsawon fiye da mintuna tara a lokacin gudanar da aikinsa a Minneapolis cikin watan Mayun shekarar da ta gabata.

Bidiyon ya nuna yadda lamarin ya faru wanda ya haifar da babbar zanga-zanga kan nuna kin jinin wariyar launin fata a fadin duniya.

A ranar Litinin ne, lauyan Mista Chauvin Eric Nelson ya yi kira ga masu taimaka wa alkalin da su yi tambaya game da harbin Daunte Wright don gano ko abin da suka ji ka iya shafar sakamakon hukuncin nasu.

Ya sake jaddada kiransa na a kebanta masu taimaka wa alkalin daga mutanen, amma alkalin Peter Cahill ya ce za a fara hakan ne kawai a lokacin da aka kai matakin karshe na shari'ar.

Mahukuntan tsaro sun fara daura damarar ko-ta-kwana ko da za a samu yiwuwar tarzoma bayan alkalan sun kai ga yanke hukuci.

Mutuwar George Floyd ta haifar da gagarumar zanga-zanga a fadin birnin, akasari ta lumana amma kuma wasu munana bayan da aka lalata daruruwan gine-gine.

Source: BBC