Jami'an diflomasiyyar kasashen waje sun nuna rashin jin daɗi kan matakin da gwamnatin Najeriya ta ɗauka na dakatar da shafin Twitter a ƙasar.
A wata sanarwar haɗin gwiwa da ƙasashen Amurka da Tarayyar Turai, da Birtaniya da Kanada da jamhuriyar Ireland su ka fitar, sun ce 'yancin faɗar albarkacin baki ɗaya ne daga cikin shika-shikan mulkin dimukradiyya a Najeriya da sauran ƙasashen duniya.
Sanarwar ta ce dakatar da shafin Twitter da hukumomin Najeriya suka yi ba shi ne matakin da ya dace a dauka ba, saboda kasar na bukatar magance matsaloli domin cimma haɗin kai da zaman lafiya tsakanin al'ummominta.
Sai dai a nata bangaren, gwamnatin ƙasar ta kare matakin da cewa, an ɗauke shi ne saboda yadda ake amfani da shafukan sada zumunta na Twitter wajen yaɗa labaran ƙarya da ke haddasa rashin zaman lafiya a ƙasar.