Menu

ECOWAS ta dakatar da Mali saboda juyin mulki a karo na biyu

 118735063 9a63ad17 C6d3 47ef B89f 622caeeecfad Shugabannin kungiyar kasashen yammacin Afurka ECOWAS bayan taron su a Ghana

Tue, 1 Jun 2021 Source: BBC

Shugabannin kungiyar kasashen yammacin Afurka ECOWAS, sun dakatar da kasar Mali daga cikinsu, bayan juyin mulkin da sojoji suka sake yi a karo na biyu cikin watanni tara a makon da ya wuce.

Jagoran juyin mulkin Kanar Assimi Goita ya ayyana kan shi a matsayin shugaban riko, sannan ya halarci tarn da ECOWAS ta yi a birnin Accra na kasar Ghana.

Ministar harkokin wajen Ghana Shirley Ayorkor Botchwey, ta shaidawa manema labarai cewa kungiyar ta yi kira ga Mali ta gaggauta zabar sabon firai minista farar hula.

Sun kuma bukaci shugabannin mulkin sojin su tabbatar sun muntunta yarjejeniyar da aka cimma ta gwamnatin riko ta jagoranci kasar na watanni 18 da kuma shirya zabe a watan Fabrairun shekara mai zuwa.

Ghana ta ce rashin zaman lafiya a Mali babbar barazana ce ga sauran kasashen yankin, wanda ke fama da matsalar masu tada da kayar baya.

A ranar Litinin din makon da ya wuce ne Kanar Assimi Goita ya sake jagorantar juyin mulki a karo na biyu, tare da kama shugaban rikon Mali Bah Ndaw, da kuma Firai minista Moctar Ouane.

Wasu rahotanni sun ce ya dauki matakin ne saboda sauye-sauyen da aka yi a gwamnati da nada sabbin mukamai ba tare da an tuntube shi ba.

Tun bayan hambarar da gwamnatin shugaba Keita, Mali ta shiga halin rashin tabbas, farar hula ba su daina bore ba kan rashin gamsuwa da yadda ake tafiyar da kasar, tare kuma ta kiran lallai a sanya lokacin zabe domin maida kasar tafarkin dimukradiyya.

Source: BBC