BBC

Actualités

Sport

Business

Culture

TV / Radio

Afrique

Opinions

Pays

MenuAfrique
BBC

Eden Hazard: Dan wasan ya nemi afuwa kan dariyar da ya yi bayan an fitar da su

 118418028 Gettyimages 1232713677 A shafinsa na Istagram Harzard ya rubuta cewa "ba ni da niyyar batawa magoya bayan Real Madrid."

Fri, 7 May 2021 Source: BBC

Dan wasan gaba na Real Madrid Eden Hazard ya bai wa magoya bayan kungiyar hakuri game da dariyar da ya yi bayan an cire kungiyar daga Champions Lig.

An ga tsohon dan wasan na Chelsea mai shekara 30 na wasa da dariya da tsofaffin abokan taka ledarsa bayan an tashi daga wasa.

A shafinsa na Istagram Harzard ya rubuta cewa "ba ni da niyyar batawa magoya bayan Real Madrid."

An cire Hazard ne kafin a tashi daga wasan bayan ya gaza tabuka komai a kwallon, wanda Madrid ta sha kashi da ci biyu babu ko daya wanda hakan ya kai sakamkon wasan 3-1 ba ki daya.

Hazard da ya bar Stamford bridge a 2019, na ta fama da suka daga magoya bayan Real Madrid saboda rashin kokari kamar yadda suka yi tsammani, wasu ma na kiran cewa a sayar da shi.

Dan wasan ya taimaka wa Chelsea wadda za ta buga wasan karshe da Manchester City a gasar zakarun Turai, ta lashe Premier biyu da Europa biyu.

Dan kasar Belgium din wanda ya zira kwallo hudu kacal a wasa 40 da ya buga wa Real, ya ce "ko da yaushe burina na bugawa Real Madrid wasa kuma na zo nan ne domin samun nasara".

Su ne dai na biyu a jadawalin La Liga, yayin da wasa hudu ya rage a gama gasar, inda Atletico Madrid ta ke samansu da maki biyu kawai.

Source: BBC