BBC

Actualités

Sport

Business

Culture

TV / Radio

Afrique

Opinions

Pays

MenuAfrique
BBC

Eid el Fitr: Hotunan yadda aka yi sallar Idi a Najeriya

 118491838 183640269 1950734375091872 1173344051706337443 N 1 Shugaba Buhari ya yi sallan Idi a fadarsa a Abuja

Sat, 15 May 2021 Source: BBC

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmed Lawan da shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila wasu jami'an gwamnati suna sallar Idi a Fadar Shugaban kasa ranar Alhamis...



A gefe daya, Aisha Buhari da wasu daga cikin 'ya'yanta mata sun bi sahu a masallacin da ke Fadar shugaban kasa



Babban masallacin Juma'a na Abuja ya yi cikar-kwari da masallata wadanda ke jira a tayar da sallar Idi



Gwamnan jihar Kaduna, Nasir Elrufai (tsakiya) tare da Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli da Sanata Uba Sani da wasu manyan mutane a filin Idi da ke birnin Kaduna...



Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje (dama) da Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a yayin da suke jirar tayar da sallah a babban masallacin Idi na kofar Mata ...

Source: BBC