Barcelona ta dauki dan wasa na uku cikin mako daya, bayan da ta dauko mai tsaron baya, Emerson Royal daga Real Betis.
Tun farko Emerson, mai shekara 22 ya je Barcelona daga kungiyar Brazil, Atletico Mineiro a Janairun 2019 kan yarjejeniya uku da ta hada da Betis a ciki.
Hakan ne ya sa dan kwallon ya je ya buga wa Real Betis wasannin aro, yanzu kuma Barcelona za ta amfana da shi.
Kuma Barcelona ta bukaci dan wasan na Brazil ya koma Camp Nou ne daga cikin kwantiragin da suka amince tun farko.
Tun farkon makon nan Barcelona ta cimma yarjejeniyar daukar Sergio Aguero da kuma Eric Garcia dukkansu daga Manchester City.
Dan wasan Argentina, Aguero da na Sifaniya, Garcia, za su koma Camp Nou da zarar yarjejeniyarsu ta kare a karshen watan nan a Etihad.
Haka kuma ana alakanta dan kwallon Liverpool, Georginio Wijnaldum da cewar zai koma Barcelona da zarar kwantiraginsa ya kare a karshen watan nan a Anfield.
Emerson ya buga wa Real Betis karawa 79 ya ci kwalllo biyar ya kuma bayar da 10 aka zura a raga.
Dan kwallon ya taka rawar gani a kakar da ta kare a Betis, wadda Manuel Pellegrini ke jan ragama da ta yi ta shida a La Liga da hakan ya sa za ta buga Europa League a badi.
Emerson ya wakilci Brazil a wasannin matasa 'yan kasa da shekara 20 da ta 23, ya kuma buga wa babbar kungiya wasan farko cikin Nuwambar 2019.