Menu

Europa League: Villarreal za ta buga Champions League a 2021/22

 118697064 Unaiemery Unai Emery kocin Villareal

Thu, 27 May 2021 Source: BBC

Kungiya biyar ce za ta wakilci Sifaniya a gasar Champions League ta kakar 2021/22, bayan da Villareal ta lashe Europa League ranar Laraba.

Villareal ta samu wannan damar bayan da ta doke Manchester United da ci 11-10 a bugun fenariti, bayan da suka tashi wasa 1-1.

Wadanda za su wakilci Sifaniya a Champions League a badi sun hada da Atletico Madrid da Real Madrid da Barcelona da Sevilla da kuma Villareal.

Ana sa ran za a sa saka Villareal cikin tukunyar farko a lokacin da za a raba jadawalin wasannin rukuni tare da Atletico da Bayern Munich da Manchester City da Inter da Sporting da Lille da ko dai Zenit ko kuma Chelsea.

Villareal wadda ta karkare La Liga ta bana a mataki na bakwai ta samu gurbin Europa Conference League tun farko, amma tunda ta ci Europa ba za ta buga gasar ba.

Haka kuma babu wata kungiyar Sifaniya da za ta maye gurbinta.

Atletico Madrid ce ta lashe La Liga na kakar nan, sannan Real Madrid wadda ba ta lashe kofi ba a kakar nan ta yi ta biyu, sai Barcelona ta uku, wadda ta lashe Copa del Rey, sai Sevilla ta hudu.

Ranar 11 ga watan Agusta za a buga wasan UEFA Super League, inda Villareal za ta jira wadda ta yi nasara tsakanin Manchester City da Chelsea.

City za ta buga wasan karshe a Champions League a karon farko da za ta kara da Chelsea ranar 29 ga watan Mayu a Portugal.

Source: BBC