Ramadan wata ne da ake son Musulmi ya siffantu da bautar Allah a koda yaushe
Ramadana wata ne mai alfarma da Musulmai ke shafe tsawon watan suna Ibadar azumi, ɗaya daga cikin daya da cikin shika-shikan Musulunci.
Wata ne da ake son Musulmi ya siffantu da bautar Allah da addu'o'i tare da neman gafara ga Mahalicci.
Watan Ramadan baki ɗayansa na ƙunshe da falala tun daga 10 na farko na watan zuwa 10 na tsakiya da kuma kwanaki mafi daraja a 10 ta ƙarshe.
Shiekh Abubakar Baban Gwale ya yi wa BBC bayani kan falalar 10 ta tsakiya da kuma abubuwan da ake son Musulmi ya himmatu.
Malamin ya ce watan Azumi wata ne da ake ƙara alherin mumuni a cikinsa - duk lokacin da aka ƙara kwanaki alherinsa yana kara ƙaruwa.
"Manzon Allah (SAW) ya ce farkon watan Ramadan rahama ne, tsakiyarsa kuma gafara ce ƙarshensa kuma 'yanta mutum ne daga wuta."
Malamin ya ce idan aka shiga zango na gafara ba wai ana goge rahama ba ne - ana son mutum ya nunka ibada domin ya hada rahama da kuma gafara tare da kara kusanci ga Allah.
Ci gaban kwanakin Ramadan ƙarin samun falala ne da kuma kusantar dare mai albarka na Laylatul kadri.
Ayyukan Ibadah da ake son mutum ya dage
Shiekh Abubakar Baban Gwale ya bayyana ayyukan Ibadah da ake son mutum ya dage akansu kamar haka: