Menu

Fira ministan Ivory Coast ya mutu

 117523595 9808ef42 00a1 40d7 9984 Cb00f40013a2 Hamed Bakayoko ya mutu ne sakamakon cutar kansa

Thu, 11 Mar 2021 Source: BBC

Gwamnati ta ce Hamed Bakayoko ya mutu ne sakamakon cutar kansa lokacin da yake neman magani a Jamus - ƙasar da aka mayar da shi kwana huɗu da suka wuce bayan an ɗauke shi daga wani asibitin Faransa.

Mutuwar Bakayoko ta kiɗima ƙasar don kuwa shi ne Fira minista na biyu da ya mutu a kan mulki cikin ƙasa da shekara.

Hamed Bakayoko ya rasu ne a ranar Laraba a birnin Freiburg na ƙasar Jamus, inda aka yi masa aiki yana da shekara 56.

An mayar da fira ministan can ne daga Faransa saboda jikinsa ya ƙara tsanani cikin 'yan kwanakin nan.

Ya dai yi fama da cutar korona a bara. Da farko ya kwanta jinya ne a Paris ƙarshen watan Janairu inda likitoci suka yi masa gwaje-gwaje a wani asibitin Amurka.

Ba a yi ƙarin bayani game da abin da aka yi masa gwaji ko magani a kai ba.

Shugaba Alassane Ouattara ya ziyarce shi a asibiti farkon wannan wata inda ya nuna damuwa game da lafiyar Fira ministan.

Ya kuma naɗa Patrick Achi, babban sakataren fadar shugaban ƙasa a matsayin fira ministan riƙo.

Bakayoko shi ne fira minista na biyu da ya mutu a kan mulki cikin ƙasa da shekara ɗaya bayan magabacinsa Amadou Gon Coulibaly, mutumin da aka tsara zai gaji Ouattara, wanda kwatsam ya faɗi ya mutu sanadin ciwon zuciya watanni ƙalilan kafin babban zaɓen Ivory Coast.

Shugaba Ouattara ya wallafa saƙon ta'azziya a shafinsa na Facebook yana cewa marigayin ya hidimtawa Cote D'Ivoire cikin jajircewa ba tare da nuna son zuciya ba.

Kuma gagarumin ɗan kishin ƙasa ne abin koyi ga matasa, kuma mutum ne mai ɗumbin karimci da riƙe alƙawari abin misali

Ya rasu ne bayan ya koma daga jinyar wata uku da ya yi a Paris inda aka yi magani kan matsalolin zuciya. Hamed Bakayoko ƙusa ne a gwamnatin Alassane Ouattara.

Source: BBC