Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi gargadi cewa wata sabuwar gwamnatin haɗin kai da ake son kafa wa a kasar za ta zama babban hatsai ga tsaron kasar.
Ya bukaci 'yan siyasa masu ra'ayin riƙau da su kauce wa shiga sabuwar gwamnatin da Naftali Bennett ke son jagoranta tare da Yair Lapid mai sassaucin ra'ayi.
Mista Lapid na da kwanaki biyu ya kafa sabuwar gwamnatin hadin kai.
Idan ya sami nasara, matakin zai kawo karshen mulkin Mista Netanyahu na firaministan da yafi dadewa bisa karagar mulki a tarihin kasar.
Hukumomin shari'a a Isra'ila na tuhumar Mista Netanyahu da aikata laifukan cin hanci da rashawa, kuma tuni yake fuskantar shari'a.
A watan Maris jam'iyyarsa ta gaza samun isassun kuri'un da zai iya kafa gwamanti ba tare da ya nemi goyon bayan wasu jam'iyyun siyasa ba.
Wannan ne kokari na hudu da kasar ta yi na aben gwamanti a shekara biyu, kuma a dukkan lokutan, sakamakon iri daya ne.
Mista Lapid ya taba rike mukamin ministan kudi, kuma an ba shi zuwa laraba 2 ga watan Yuni ya kafa sabuwar gwamnati. Jam'iyyarsa ta Yessh Atid ce ta zo ta biyu, inda jam'iyyar Mista Netanyahu ta Likud ta zo ta ɗaya a zaben da aka yi na baya-bayan nan.