Menu

Ghana: Yadda aka kama mutumin da yake tsafi da gawar mace

 116334591 Gettyimages 855075848 594x594 'Yan sanda sun kama matsafi da yake sanya matasa su kai masa gawarwaki

Fri, 9 Apr 2021 Source: BBC

'Yan sanda a Ghana sun kama wani matsafi da yake sanya matasa su kai masa gawa, domin hada maganin da za su zama masu kudi.

Rahotanni sun ce an cafke shi ne a yankin Amanase da ke yammacin kasar inda ya ɓuya.

Matasan biyu da ake zargin sun hada da Felix Nyarko, mai shekara 16, sai Nicholas Kiki, dan shekara 18, sun bayyana wa 'yan sanda cewa wani matsafi da suke gani a talabijin ne ya umarce su su kai gawar mace da kudin cedi 5,000 domin a yi musu kudi.

Sai suka shirya yadda za su sace yaron, Ishmael Mensah tare da bukatar mahaifiyarsa ta biya su cedin kasar Ghana 5,000.

Wannan kamen na zuwa ne bayan kama wasu matsafa da ake ganin suna bai wa matasa ƙwarin gwiwar yin ayyukan assha.

Don haka matakin da shari'a za ta dauka a kan matasan da matsafan zai zama izina ga 'yan baya.

Kotun gundumar Ofankor na tsare da su, za kuma su bayyana gabanta a ranar 20 ga watan Afirilun 2021.

Mutuwar yaro mai shekara 11 ta fusata al'umma a kasar Ghana, tare sukar matsafa da ke tallan ayyukansu a gidajen talabijin din kasa.

An kara matsa wa gidajen talabijin lambar su daina watsa irin tallace-tallacen, waɗanda suke sanya matasa aikata muggan laifuka.

Tsohon shugaban Ghana John Agyekum Kufuor ya shiga gangamin, tare da kira ga shugabannin da kafafen yada labarai, su daina bai wa irin mutanen filin tallata mummunar dabi'arsu.

Mahaifin Ishmael Mensah ya sha alwashin yin gaban kansa a hannunsa matukar kotu ba ta yanke wa wadanda suka janyo mutuwar dansa hukunci daidai da laifin da suka aikata ba.

Iyayen yaron da suka kasance Musulmai, sun yi kira ga hukumomi su ba su gawar ɗansu domin yi masa sutura da binne shi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, wanda ya kamata a ce an binne shi tuntuni.

Source: BBC