Wani garken giwaye da suka yi zuga domin tafiya wani tattakin bazata, na tsawon kilomita 500 (mil 300) ya isa wani birni a ƙasar China inda miliyoyin mutane ke rayuwa.
Giwayen su 15 sun yi ta awon gaba da shukoki da kuma kutsa kai gidajen mutane a tafiyar tasu daga gundumar kudancin Yunnan zuwa babban birnin yankin Kunming.
Ana kan yin wani babban yunƙuri na samar da tan-tan na abinci don ƙoƙarin ajiye su cikin ƙoshin lafiya.
Ba a san dalilin da ya sa suka bar matsuguninsu, suka fara tattakin ba, wanda ya ja hankalin mazauna garuruwa da masana.
Wasu mutane sun ce wataƙila wani jagora mara gogewa ne ya sa garken ya yi ɓatan kai, yayin da wasu suka yi imanin cewa babu mamaki giwayen suna neman sabon matsuguni ne.
Giwar yankin Asiya nau'in giwa ce da ke fuskantar barazanar ɓacewa a ban ƙasa. China tana da giwayen sake kimanin 300 ne kawai, kuma galibinsu a gundumar kudancin Yunnan suke.
Masana kimiyya sun ce wannan ita ce tafiya mafi nisa da wata giwar sake a wajen ta taɓa yi daga matsuguninta.
Jaridar Kunming Daily ta ce biranen Kunming da Yuxi sun tura ƴan sanda da ma'aikatan gaggawa kimanin 700 ɗauke da tan goma na masara da kankana da kuma sauran kayayyakin abinci.
Suna samun rakiyar motocin dakon kaya da jirage marasa matuƙa domin yin ƙoƙarin karkata akalar dabbobin zuwa tafarkin da ba za su cutu ba.
Kar ku yi kallon banza ko ku bar masara ko gishiri a waje; ku tsaya can nesa da su kuma kar ku dame su da wasan wuta, an gaya wa mazauna garuruwa.
Tafiyar ta ƙunshi bi ta cikin gonaki, da labika da kuma kwalta kuma ta ci gaba dare rana.
Masana dabbobi sun ce kamar dabbobin sun ƙara sauri, wataƙila saboda dandazon mutane ya ƙara fargabarsu kuma mawuyaci ne giwayen su yi yunƙurin shiga Kunming.
Ƙoƙarin a juya da su ya ci tura, kuma wataƙila masana kimiyya su yi ƙoƙarin nema musu wajen da zai dace su rayu.
Labarin Bulaguron
Babu cikakkiyar masaniya game da lokacin da garken ya bar gida, wanda bisa ga dukkan alamu gandun daji na Mengyangzi a Xishuangbanna, a Kudu maso yammacin Yunnan ne.
An sanar da mahukunta a karon farko game da tattakin nasu ne lokacin da mutanen yankin suka hango garken kimanin kilomita 100 kudu da Xishuangbanna a watan Afrilu.
Akwai tunanin giwayen su 17 ne tun da farko, amma bisa ga dukkan alamu biyu suka juya da suka kai yankin Mojiang.
Wasu rahotanni sun ce su 16 asali amma ɗan da aka haifa ya sa adadin ya dawo 15 bayan biyun sun juya.
Game da tafiyar, ta haɗa da gaurayen ratsa gonaki da labika da kwalta kuma ta ci gaba dare da rana.
A wani lokaci, garken ya bi wata babbar hanya ta cikin ƙauyen Eshan kuma kamar sun buga wa mutanen garin ƙofofinsu.
Wani hoton bidiyo a kafofin sada zumunta ya nuna mutane na gudu zuwa kan titi suna ihu cewa "suna zuwa", bayan haka kaɗan sai motar ƴan sanda da kuma giwayen suka biyo baya, kamar yadda Jaridar The South China morning Post ta rawaito.
Wata sanarwar gwamnatin Yunna A ƙalla giwa ɗaya ta bugu da n ta ce garken ya jawo matsala sau 412.
Labarai sun gabata,har da na wani mutumin da ya manyanta, Wanda kafar Tashar Jimu news ta ce ya ɓuya a ƙarƙashin gadonsa a gidansa da yake zama da ya yi ritaya, yayin da hancinan Giwa suka kutsa cikin ɗakuna.
A ƙalla giwa ɗaya ta bugu sakamakon wani jiƙon hatsin da ya yi tsami da ta sha,a wani rahoto da ke da wuyar tabbatarwa.
Kuma sun lalata shukoki da kuɗinsu ya kai fiye da Dala Miliyan ɗaya (£710,000) a kan hanya, amma an yi sa'a babu wanda ya ji rauni.
Wani rahoto ya ce garken ya ƙunshi mata shida da maza manya guda uku da matasa uku da kuma ƙanana uku.
Me ya sa suka baro inda suke?
Akwai wasu wasannin barkwanci a kafofin sada zumunta a China. Wani saƙo a kafar sada zumunta ta Weibo ya ce wataƙila giwayen na son halartar babban taron Majalisar Dinkin Duniya a kan ire-iren halittu a Kunminng.
Sun yi sammako ne, saboda taron ba zai kankama ba sai a watan Oktoba.
Amma fa wannan babban al'amari ne da ya shafi rasa muhalli da da ƙaruwar arangama tsakanin giwaye da manoma a Yunnan.
Li Zhongyuan, wani jami'i a gandun daji na Xishuangbanna ne, ya gaya wa Global Times cewa abincin da giwayen suka saba ci ya ƙare a matsuguninsu, inda yanzu suka koma cin kayan gona kamar masara da rake
Za a iya samun wasu tattakin idan matsugunan suka ci gaba da raguwa, ta hanyar shuka roba da sauran shuka masu kawo kuɗi.