Menu

Gomman mutane sun jikkata a rikicin Birnin Kudus

 118164973 3f3f924f 2070 4c41 Ae6b 588247fb5466 Ana ci gaba da arangama tsakanin jami'an tsaron Isra'ila da Falasdinawa

Sat, 24 Apr 2021 Source: BBC

Can a gabashin birnin Kudus ana ta arangama tsakanin jami'an tsaron Isra'ila da Falasdinawa, yayin da jami'an tsaron ke kokarin hana 'yan kungiyoyin kishin Yahudawa kaiwa ga Falasdinawan inda ake kara samun zaman dar-dar da neman ba-ta-kashi tsakanin bangarorin biyu.

Daruruwan matasa ne daga kungiyoyin kishin Yahudawa ke kururuwa da kiran ramuwar gayya, da kiran mutuwa a kan Falasdinawa yayin da suke tattaki a titunan tsohon birnin na Kudus.

Tsawon kwanaki wannan wuta na ta ruruwa a titunan birnin na Kudus, bayan fadace-fadace na wariyar jinsi tsakanin bangarorin biyu. Wasu Falasdinawa sun dauki hoton kansu a lokacin da suke kai wa wasu 'yan addinin gargajiya naYahudawa hari, suka kuma sanya hotunan bidiyon a shafin intanet na Tik Tok.

Yayin da su kuma wasu masu tsananin kishin Yahudawa ke kai hari da farma Falasdiwan, amma kuma jami'an tsaro na kokarin shiga tsakani.

Haka kuma 'yan sanda na ke kokarin hana Yahudawan kaiwa ga kofar birnin da ake kira Damascus Gate, inda ake dauki-ba-dadi tsakanin Falasdinawa da jami'an tsaron Israil'a.

An kai sati biyu ana rikici kan neman shiga wata matattara da Musulmi kan hadu a wannnan lokaci na azumin Ramadana.

Kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ta ce an raunata Falasdinawa akalla dari daya wadanda suka hada da 21 da ke bukatar a kai su asibiti domin yi musu magani.

An kuma kama mutane da dama a rikicin, wanda a ranar Alhamis Falasdinawa suka zargi 'yan sanda da kokarin hana su zuwa wannan fitaccen wuri da ke wajen Kofar Damascus kamar yadda suka saba yi a duk lokacin azumin Ramadana.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito wani jami'in 'yan sanda na Isra'ila na cewa za su dauki tsattsauran mataki a kan duk wanda ya nemi tayar da hankali ko bore

Matsayin birnin Kudus shi ne babban abin da ke haddasa rikici tsakanin Isra'ila da Falasdinawa. Kuma birni ne mai matukar muhimmanci da ke da wuraren ibada na tarihi ga addinin Yahudawa da Musulmai da kuma Kiristanci, musamman ma bangaren gabashin.

Isra'ila ta mamaye tare da kwace wannan bangare a yakin Gabas ta Tsakiya a 1967 wanda a da yake karkashin ikon Jordan, ta kuma dauki birnin gaba daya a matsayin babban birninta ita kadai, wanda ba za ta yadda ta raba da Falasdinawa ba.

Su kuma Falasdinawa sun kafe cewa Gabashin Kudus shi ne zai zama babban birnin kasar da suke fafutukar kafawa, kuma duk wata tattaunawa kan rikicinsu na Isra'ila a nan gaba sai ta shafi matsayin yankin.

Source: BBC