Manchester City ta kai wasan daf da karshe a gasar Champions League, bayan da ta doke Borussia Dortmund da ci 2-1 da suka kara ranar Laraba.
Minti 15 da take leda Dortmund ta ci kwallo ta hannun Jude Bellingham, kuma haka suka je hutun rabin lokaci.
Bayan da suka koma karawar zagaye na biyu ne City ta farke ta hannun Riyad Mahrez a bugun fenariti, sannan Phil Foden ya ci na biyu saura minti 15 a tashi daga fafatawar.
A wasan farko da suka buga a makon jiya City ce ta yi nasara da ci 2-1, kungiyar ta Ettihad ta kai zagayen daf da karshe a gasar ta Zakarun Turai da kwallo 4-2 gida da waje kenan.
Wannan ne karo na bakwai da Pep Guardiola ke kai wa matakin daf da karshe a gasar Champions League da ya lashe kofi biyu a Barcelona daga ciki.
Tun bayan da kocin ya bar kungiyar Camp Nou a kakar 2012 bai sake daukar kofin a Bayern Munich ba a shekara ukun da ya yi a Jamus.
Kocin dan kasar Spaniya ya karbi ragamar jan Manchester City a kakar 2016, bai taba zuwa karawar karshe ba a kungiyar ta Etihad da ta Jamus ba.
Kokarin da Guardiola ya yi a kungiyar ta Ingila shi ne zuwa karawar daf da karshe a bara, bayan da ya yi nasara a kan Real Madrid daga baya Lyon ta yi waje da shi.
Manchester City na fatan lashe kofin Premier League a bana, bayan da take ta daya a kan teburi da tazarar maki 11 tsakaninta da Manchester United.
City ta kai wasan daf da karshe a FA Cup, za ta buga wasan karshe da Tottenham a Caraboa Cup ta kuma kai daf da karshe a Champions League na bana.
Kokarin Guardiola a Champions League
A kungiyar Barcelona:
2008-09 Ya lashe kofin Barcelona 2-0 Man Utd
2009-10 Wasan daf da karshe Barcelona 2-3 Inter (gida da waje.)
2010-11 Ya lashe kofin Barcelona 3-1 Man Utd
2011-12 Wasan daf da karshe Barcelona 2-3 Chelsea (gida da waje.)
A kungiyar Bayern Munich
2013-14 Wasan daf da karshe Bayern 0-5 Real Madrid (gida da waje.)
2014-15 Wasan daf da karshe Bayern 3-5 Barcelona (gida da waje.)
2015-16 Wasan daf da karshe Bayern 2-2 Atletico Madrid (gida da waje.)
A kungiyar Manchester City
2016-17 Zagayen kungiyoyi 16 Manchester City 6-6 Monaco (gida da waje.)
2017-18 Zagayen quarter final Manchester City 1-5 Liverpool (gida da waje.)
2018-19 Zagayen quarter-final Manchester City 4-4 Tottenham (gida da waje.)
2019-20 Wasan daf da karshe Manchester City 1-3 Lyon (gida da waje.)