Menu

Gwamnatin Najeriya na nazarin zabtare albashin ma’aikata

 118380459 28e2aee5 1f40 4eef Aca3 50635376cde4 Gwamnatin tarayya na kuma son ta rage yawan hukumomi da ma'aikatun gwamnati

Thu, 6 May 2021 Source: BBC

Gwamnatin Najeriya tana nazari kan albashin ma'aikata da kuma rage yawan hukumomi da ma'aikatun gwamnati.

Ma'aikatar kuɗi da kasafi da tsare-tsare ta ce an kafa kwamiti da zai yi nazarin yadda za a rage yawan kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa musamman zabtare albashi da kuma rage yawan hukumomi.

An ambato ministar kuɗin Najeriya Zainab Ahmed na cewa, dole ne a fito da hanyoyin warware matsalar ƙarancin kuɗi da gwamnati ke ciki, lura da irin tsare-tsaren da ta ɗauko da kuma lalurorin yau da kullum da ta ke magancewa kamar albashi da sauran kuɗaɗen tafiyar da gwamnati.

Mai magana da yawun ma'ikatar kuɗin ta Najeriya Yunusa Tanko Abdullahi ya shaida wa BBC cewa gwamnati za ta yi aiki da shawarwarin rahoton kwamitin Oronsaye wanda tsohuwar gwamnatin Jonathan ta kafa.

Rahaton Oronsaye ya bayar da shawarar rage yawan hukumomi da ma'aikatu saboda sun yi yawa domin rage yawan kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa.

Shugaban ƙasa ya ce a diba a san me za a yi - akwai ma'aikau da yawa da ke biyan albashi da ya fi na wasu ma'aikatu, ana son a tace a raba albashin da wasu suke karɓa ya kasance an ba mutane da yawa maimakon ƴan ƙalilan," in ji Yunusa Tanko Abdullahi.

Amma ya ce an kafa kwamitin da zai tantance ya tace hukumomi ko ma'aikatun da za a rage kuma kwamitin zai tura wa shugaban kasa shawarwarinsa daga nan shugaban ya ɗauki mataki.

An shiga yanayi ne ?

An daɗe da aka gabatarwa gwamnatin Najeriya da shawarwarin rahoton kwamitin Oronsaye da aka kfa tun a 2011.

Gwamnati kuma a cewar mai magana da yawun ma'ikatar kuɗin Yunusa Tanko Abdullahi "a yanzu an shiga wani yanayi na ƙoƙarin da gwamnati ke yi na biyan albashi da kyar."

Annobar korona ta haifar faɗuwar farashin mai da rashin kasuwa wanda ya sa dole gwamnati ta sake lale - kuma kasafin kuɗinmu ya samu giɓi," in ji shi.

Ministar kuɗi Zainab Ahmed ta ce gwamnatin tarayya ta aminta da kasafin kudin na kusan naira tiriliyan 14, dogaro da hasashen samun kudin shiga kusan tiriliyan takwas.

Akan haka ta ce mafita ɗaya ita ce yanke kuɗaɗen ayyukan da ba su da muhimmanci sosai, da kuma hade wasu ma'aikatun da wasu, a kuma soke ayyukan da za a iya tafiyar da gwamnati ba tare da su ba.

Ministar ta ce su kansu ma'aikatun da ke da matuƙar muhimmanci akwai bukatar su zauna da ita don duba yiwuwar yanke wani kaso na kuɗaɗen da suke kashewa.

An kuma ambato ministar na cewa wani abu da ke damunta shi ne akwai ayyukan da duk shekara da ake gani a kasafin kuɗi bayan tuni an biya kudaden kammala su, da kuma yadda ake tsula kuɗaɗe ga wasu ayyukan da ba su da wani tasiri ga talaka.

Albashin ƴan majalisa fa?

Zabtare albashi ma'aikata zai iya sake haifar maharawa tsakanin ƴan Najeriya da suka daɗe suna yi kan maƙudan kudaden da suke zargin gwamnati na kashewa ƴan majalisa.

Kamar yadda gwamnatin Najeriya ta ce zabtare duk wani abu marasa amfani daga cikin kasafin a matsayin wani mataki na rage kudin gudanar da mulki a kasar, wasu za su yi tunanin matakin zai shafi albashin ƴan majalisa.

Sai dai ma'aikatar kuɗin Najeriya ta ce taɓa albashin ƴan majalisa ya dogara da shawarwarin da kwamitin da aka kafa ya gabatar wa shugaban ƙasa.

Shugaban hukumar ICPC Bolaji Owasanoye wanda ya jagoranci tattaunawar ya ce irin makuɗan kuɗaɗen da ma'aikatu ke karba da sunan gudanarwa shi ne babban dalilin cin hanci da rashawa a Najeriya tun inda aka fito.

A cewarsa da dama ana fakewa ne da irin wa dannan kuɗaɗe wurin talauta gwamnati.

Source: BBC