Menu

Hare-hare 'ƴan bindiga da tsadar abinci sun jefa manoman Najeriya cikin 'tsaka mai wuya'

 118175214 Gettyimages 460594127 Rashin tsaro da tsadar abinci sun jefa manoman Najeriya cikin 'tsaka mai wuya'

Sat, 24 Apr 2021 Source: BBC

Latsa hoton sama domin sauraren rahoton Awwal Janyau



Ga lokacin damina ana tunkara, a lokacin da ake fuskantar tsadar kayan abinci da hare-haren ƴan bindiga masu kashewa da satar mutane, al'amarin da ya jefa manoma a arewacin Najeriya cikin tsaka mai wuya.

Noma kamar wajibi ne musamman ga mutanen karkara domin samun abinci da kuma samun kuɗaɗen shiga.

Amma yanzu harkar noma ta shiga wani mawuyacin hali sakamakon hare-haren yan bindiga baya ga ƙalubale da annobar korona ta haddasa.

Hare-haren yan bindiga da masu fashin daji a ƙauyukan jihohin arewa maso yammacin Najeriya musamman Zamfara da Katsina da yankin Birnin Gwari a Kaduna ya tilastawa ɗaruruwan manoman kauracewa gonakinsu.

Manoman sun warwatsu zuwa wasu manyan birane domin samun mafaka.

Duk da wasu sun koma kauyukansu saboda sulhun da gwamnati ta ce ta yi da yan fashin daji da suka addabe su, amma akwai waɗanda suka haƙura da manyan gonakinsu a kauye kuma suke fargabar komawa gida, matakin da ke ƙara haifar da barazanar ƙarancin abinci.

A wani rahoton da ta fitar a makon da ya gabata, hukumar samar da abinci ta duniya, WFP ta ce yunwa za ta tsananta tsakanin watan Yuni zuwa Agusta na wannan shekarar 2021.

Rahoton WFP ya ce fiye da mutum miliyan 31 a yankin yammacin Afirka za su fuskanci barazanar yunwa sakamakon tsadar kayan abinci da kuma rikici da matsaloli na tsaro.

"Lokaci ne da abinci zai yi wahala kafin zuwa lokacin girbi," a cewar rahoton.

Ga abubuwa uku da suka jefa manoma cikin tsaka mai wuya:

Tasirin hare-haren ƴan bindiga

Rashin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali musamman a jihohin arewa maso yammacin Najeriya ya sa har yanzu manoman da suka yi gudun hijira ba su koma ga gonakinsu ba, matakin da ya rage yawan abincin da ake samarwa a Najeriya.

Wani manomi Isah Musa da ya yi gudun hijira daga ƙauyen Jangeme zuwa garin Gusau a jihar Zamfara ya ce kafin ya yi gudun hijira yana noma sosai wanda yake ci da iyalinsa har ya kai kasuwa ya sayar amma yanzu ba ya da halin yin noman.

"Ɓarayi suka addabe mu muka gudu, yanzu ba wani aikin da nake sai lebaranci," in ji shi.

Sarkin Noman Zamfara Alhaji Hassan Kwazo ya taɓa shaida wa BBC a watan Disamban 2020 cewa za a ɗauki shekara 10 kafin noma ya dawo daidai a jihar Zamfara saboda a cewarsa noman gaske da aka sani a Zamfara ya gagara saboda hare-haren ƴan bindiga.

"Ba a yi noman da aka saba ba kusan shekara biyar zuwa shida, noma ya ja baya a Zamfara, masu kuɗi waɗanda ke noma buhu 500 zuwa 1,000 gonakin sun gagare su zuwa."

"Kuma kafin noman ya dawo kila za a kai shekara 10 saboda duk manoman da suke noman na gaske sun watse," in ji Sarkin Noman Zamfara.

Hukumomi da jami'an tsaron sun sha iƙirarin cewa suna kokarin ganin an shawo kan matsalar da magance ta baki daya, amma har yanzu ana kai hare-hare da garkuwa da mutane duk da ikirarin gwamnatin Zamfara na yin sulhu da ƴan fashin.

Manomi idan ya samu wurin shuka da abinda zai shuka babu abin da ya ke buƙata fiye da tsaro da kwanciyar hankali.

Rashin tsaro da kwanciyar hankali ga manoman wata babbar barazana ce ga wadatar abinci a Najeriya da ma yammacin Afrika.

Tsadar kayan abinci

Yadda kayan abinci ke ƙara tsada, wani babban ƙalubale ne da ya jefa manoma cikin tsaka mai wuya.

Rashin noman zai ƙara haifar da ƙarancin abinci da kuma tsadarsa, kamar yadda yin noma zai bunƙasa abinci da rahusa.

Alkalumman da hukumar ƙididdiga ta Najeriya ta fitar a watan Maris wato NBS sun nuna an samu hauhauwar farashin da ya kai kashi 17.33 cikin ɗari a watan Fabrairun da ya wuce.

Alƙaluman sun nuna cewa tashin farashin ya ƙaru ne da kashi 1.54 a Fabrairun 2021 idan aka kwatanta da kashi 1.49 a watan Janairu.

Kuma farashin kayan abinci ya tashi da kashi 21.79 a Fabrairun da ya gabata idan aka kwatanta da kashi 20.57 a watan Janairu.

Hukumar ta ce wannan ne karon farko da aka samu irin wannan tashin farashi a cikin shekaru hudu da suka wuce.

Rahoton WFP ya ce farashin abinci ya lunlunka da sama da kashi 200 a ƙasashen yammacin Afrika, wanda yajefa masu ƙaramin ƙarfi cikin mawuyacin hali na samun abin da za su kai baka, sakamakon matakan da annobar korona ta tilasta aka ɗauka na tattalin arziki.

Rahoton ya ce an samu ƙarin kashi 30 na ƙarancin abinci fiye da bara.

Masana na ganin dalilai da yawa ne suka janyo hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya kasar da tattalin arzikinta ke dogaro da arzikin fetir.

Shuaibu Idris Mikati masanin tattalin arziki a Najeriya na ganin ba ya ga faɗuwar darajar naira, barazanar hare-haren ƴan bindiga ga manoma ya ƙara haddasa hauhawan farashin kayayyakin masarufi.

Masanin na ganin sai gwamnatoci sun ɗauki matakan gaggawa don magance yiwuwar dorewar wannan yanayi na tsadar rayuwa ta hanyar gaggauta tabbatar da tsaro ga manoma.

Barazanar ƙarancin abinci

Matsalar tsaro na daga cikin abubuwan da ake hasashen za su haddasa ƙarancin abinci a arewacin Najeriya saboda yadda yan fashin daji da masu garkuwa ke addabar manoma suna hana su nome gonakinsu

Ana ganin ƙalunbalen tsaro da manoma ke fuskanta zai yi tasiri ga samar da abinci a Najeriya.

Babban jami'in yaɗa labarai na ƙungiyar manoma ta ƙasa, Alhaji Muhammad Magaji ya ce tabbas yankin arewa maso yamma na cikin matsala.

"A yankunan Katsina kamar Ɗanmusa da Safana da Bakori da Dutsinma, suna noma abinci kusan kashi 30 zuwa 35 na abin da ake samu a arewa maso yamma gaba ɗaya."

"Amma a yanzu noman zai gagara, manoma za su kasa zuwa gona," in ji shi.

Ya ce hakan ya shafi yankunan Kaduna na Igabi da Birnin Gwari da Giwa da Kauru.

Wannan matsala suka ce za ta haifar da tsadar kayayyakin abinci a yankin arewacin Najeriya saboda rashin abincin.

Sarkin Noman Zamfara Alhaji Hassan Ƙwazo ya bai wa gwamnati shawara cewa ya kamata ta ɓullo da tsarin tallafa wa matasa na karkara, "waɗanda ke yin noma amma ake korewa daga gonakinsu kuma ake kashewa".

Ya ce manomi ba bashi yake buƙata ba, idan aka ba shi tallafi da tsaro sun ishe shi.

Source: BBC