An soma jana'izar mutanen da suka mutu sakamakon jerin fashe-fashen bama-bamai a kusa da wata makaranta a Kabul ranar Asabar, inda yanzu aka ce sun zarta mutum 50.
Bama-baman sun tashi ne a yayin da dalibai suke fita daga ginin da lamarin ya auku. Hukumomi sun ce galibin wadanda suka mutu mata ne yara.
Babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai hare-haren a Dasht-e-Barchi - yankin da masu tayar da kayar baya na mabiya Sunnah suke yawan kai wa hari.
Jami'an gwamnatin Afghanistan sun dora alhakin harin kan mayakan kungiyar Taliban, sai dai kungiyar ta musanta hannu a lamarin.
Yarinyar nan da ta samu lambar yabo ta Nobel wadda kuma take gwgwarmayar ganin 'yan mata sun samu ilimi Malala Yousafzai - wadda Taliban ta harba a ka a shekarar 2012 - ta wallafa sakon Tuwita game da harin da ta bayyana a matsayin "hari mai tayar da hankali".
"Ina bayyana jajena ga iyalan mutanen da harin makarantar Kabul ya ritsa da su," in ji ta.
Ganau da dama sun bayyana yadda bama-baman uku suka tashi, yayin da wata mata, Reza, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa ta ga "gawarwaki da dama cikin jini da cikin ƙura da hayaƙi".
"Na sa wata mata tana duba gawarwakin kuma tana kiran sunan 'yarta," a cewar Reza. "Daga nan ta ga jakar makarantar 'yarta jina-jina sai kawai ta suma da faɗi ƙasa."
Fiye da mutum 100 ne suka jikkata sanadin harin. Rahotanni daga Kabul na cewa binrin cike yake da masu sayen kayayyaki gabanin bikin sallah da ke tafe a makon gobe.
Najiba Arian, mai magana da yawun ma'aikatar ilimi, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ta ce makarantar ta gwamnati ce wadda maza da maza suke halarta. Galibin waɗanda suka jikkata 'yan mata ne, a cewar Ms Arian.