Menu

Hukumomin Najeriya ba sa abin da ya kamata don kare rayuka - Amnesty International

 118709600 Afaf4f1b D35e 4e72 88fc 81ae120a52fc Akwai tsabar gazawar hukumomin Najeriya wajen kare rayuka da dukiyar al'umma, inji Amnesty

Sat, 29 May 2021 Source: BBC

Ƙungiyar Amnesty International ta ce ƙaruwar hare-hare masu firgitarwa da satar mutane don neman fansa da yawan kashe-kashe a faɗin Najeriya, sun jefa mutane cikin rashin kwanciyar hankali.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar albarkacin cikarta shekara 60 da fara aiki a Najeriya, ta kuma ce waɗannan abubuwa na nuna tsabar gazawar hukumomi wajen kare rayuka da dukiyar al'umma.

Ƙungiyar ta ce ta fara aiki ne ranar 1 ga watan Yunin 1967 da wani ƙoƙari lokacin yaƙin basasar Najeriya ta hanyar ayyana Wole Soyinka, mutumin da ya samu kyautar Nobel, a matsayin fursunan da aka ɗaure saboda aƙidarsa.

Amnesty ta ce tsakanin 1968 zuwa 1969 rahotonta na shekara-shekara ya bayyana damuwa kan yadda ake jingina haƙƙin ɗan adam a Najeriya da sunan yaƙin basasa.

Ta kuma ce babu wani ƙwaƙƙwaran sauyi ta fuskar kare haƙƙin ɗan adam da aka samu tun daga 1967.

"Kashe-kashe ba ji ba gani da gaza kawo ƙarshensu da hukunta mutanen da ake zargi da laifi na ci gaba da zama barazana ga ƴancin rayuwa a Najeriya," in ji sanarwar ta Ammnesty.

Daraktar Amnesty a Najeriya Osai Ojigho, ta ce daga mulkin kama karya na zamanin sojoji har zuwa mulkin farar hula a yau, ana keta haƙƙin ƴan adam da kuma tozarta ƴan ƙasa.

Wasu labaran da za ku so

Takura wa ɗalibai

Amnesty ta ce a ranar 10 ga watan Afrilun 1978 an kashe ɗalibai ƴan Najeriya shida kuma an tsare wasu da dama saboda zanga-zanga kan ƙarin kuɗin makaranta.

Tun daga nan matasan Najeriya sun yi ta fuskantar dirar mikiya don kawai sun aiwatar da ƴancinsu na yin taro cikin lumana.Kama daga zanga-zangar 12 ga Yuni ta masu rajin dimokraɗiyya a 1993, da zanga-zangar a mamaye Najeriya ta 2012, zuwa zanga-zangar ta 2020, mahukuntan Najeriya sun ci gaba da murƙushe zanga-zangar lumana da ƙarfin tuwo.

Osai Ojigho ta ce zanga-zanga ba laifi ba ce kuma jazaman ne a bar ƴan Najeriya su gudanar da taruka cikin lumana, su furta albarkacin baki ba tare da fargaba ba.

Ta ce amfani da ƙarfi fiye da ƙima da ƴan sanda ke yi har yanzu matsala ce a ƙasar.

Ƙungiyar ta kuma ce fyaɗe da ƴan sanda jami'an tsaro ke yi wa mata da ƴan mata da kuma a gidajensu da garuruwansu wata annoba ce a Najeriya.

A cewarta daga shekarun 1960 zuwa yau, ayyukan ƙungiyar sun nuna cewa yayin da aka cimma nasarori a ɓangarori kamar dokar ƴancin ƙananan yara da dokar hana azabtarwa, waɗanda ake zargi na ci gaba da nuna gadara.

Rahoton ya ce gaza hukunta masu keta ƴancin ɗan adam wani tabo ne da ke ɓata mutuncin Najeriya.

Source: BBC