Fadar shugaban Najeriya ta tabatar da abin da ta kira yunkurin da wasu suka yi na fasa gidan shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa ranar Litinin.
A wata sanarwa da Malam Garba Shehu, mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa a shafinsa na Tuwita ya ce wasu sun yi yunkurin fasa gidan Mr Gambari da misalin karfe uku na dare.
Professor Gambari, whose house is on a street next to the Villa has assured that there is nothing to worry about from the incident.
— Garba Shehu (@GarShehu) May 10, 2021
"A kan wannan batu, 'yan sanda suna neman wanda ya yi yunkurin fasa gidan wani mai suna Maikano Abdullahi ba tare da nasara ba ranar Alhamis ta makon jiya.
"Maikano yana zaune a kan titi daya da Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, kusa da fadar Villa," a cewar Garba Shehu.