An haifi Idriss Deby a garin Fada da ke arewa maso gabashin Chadi a 1952.
A matsayinsa na jami'in soji, ya taimaka wa Hissen Habre wajen tumbuke gwamnatin Goukouki Oueddei a 1982.
A shekarar 1989 ya tsere zuwa Sudan bayan da aka zarge shi da yunkurin juyin mulki.
Shekara daya bayan haka, kungiyarsa ta Patriotic Salvation Movement ta hambarar da Mr Habre daga mulki a 1991 inda aka sanar da Mr Deby a matsayin shugaban kasar Chadi.
Ya yi nasara karon farko a zaben da aka gudanar a kasar a 1996 bayan an kaddamar da tsarin mulkin da ya bai wa jam'iyyu da dama tsayawa takara.
An sake zabensa a 2001, sannan zaben raba-gardamar da aka yi a watan Yunin 2005 wanda ya soke dokar wa'adi biyu ga shugaban kasar, kuma ya bai wa Deby damar sake tsayawa takara.
Shugaba Deby ya yi nasara a watan Yunin 1996.
A shekarar 2001 Mr Deby ya kara lashe zabe.
A 2005 ne kasar ta tsunduma yakin basasa tsakanin Musulmi da Kirista.
A 2006 ne aka yi yunkurin yi masa juyin mulki ta hanyar harbo jirginsa, amma hakan bai yi nasara ba.
A ranar 8 ga watan Agusta ne kuma aka kara rantsar da Deby a matsayin shugaban kasar a shekarar 2006.
An sake rantsar da shi a wa'adi na hudu a watan Afrilun shekarar 2011, bayan ya samu gagarumin rinjaye a babban zaben kasar.
Kuma a farkon wannan shekarar aka sake yi wa kundin tsarin mulkin kasar garambawul tare da mayar da da tsarin wa'adi biyu ga shugaban kasa.
Yayin da kuma ya yi rantsuwar ci gaba da mulki a karo na biyar a ranar 8 ga watan Agustan 2016.
Ya mutu ne kwana guda bayan kwarya-kwaryan sakamakon da aka fitar ya nuna cewa shi ne ya lashe zaben da aka gudanar a farkon watan Afrilu inda zai yi mulki a karo na shida.
A shekarar 2020 ne majalisar dokokin kasar ta Chadi ta amince da wata doka da ta kara wa Idriss Deby Itno girma daga Janar zuwa mukamin Marshal - wanda shi ne mukamin da ya fi kowanne a tsarin aikin soji.
Wannan karin mukami ya biyo bayan gwagwarmayar da 'yan kasar suke ganin shugaban ya jagoranta zuwa filin daga domin yin artabu da mayaka masu ikirarin Jihadi a kasar tare da tura sojojinsa zuwa Mali da Najeriya .
Irin wannan mukami ne dai marigayi Idi Ameen na Uganda da Mabutu sese seko na Zaire da kuma Jean Bedel Bokassa na jamhuriyar Afirka ta Tsakiya suka rike.