Menu

Iheanacho ya kusan kai Leicester gurbin Champions League

 118218781 Iheanacho Kelechi Iheanacho na nuna murnan sa

Tue, 27 Apr 2021 Source: BBC

Leicester City ta kusan samun gurbin shiga gasar Champions League ta badi, bayan da ta doke Crystal Palace 2-1 a wasan Premier da suka kara ranar Litinin.

Wilfred Zaha ne ya fara ci wa Palace kwallo a minti na 12 da take leda, bayan da ya samu tamauala daga wajen Eberechi Eze.

Sai dai Leicester ta farke ta hannun Timothy Castagne a minti na biyar da komawa zagaye na biyu, bayan da suka yi hutu.

Saura minti 10 a tashi daga karawar Kelechi Iheanaco ya zura na biyu a raga kuma na 12 da ya ci a Premier League a karawa tara.

Da wannan sakamakon Leicester ta ci gaba da zama ta uku a kan teburin Premier League da tazarar maki bakwai tsakaninta da West Ham ta biyar, kuma saura wasa biyar a karkare kakar bana.

Leicester wadda ta kai wasan karshe a FA Cup na bana a karon farko tun 1969 ta buga Champions League a 2016/17 har ta kai wasan quarter finals, bayan da ta lashe Premier a 2015/16.

Cikin wasa biyar da ke gaban Leicester nan gaba tana da mai zafi da Manchester United wadda take ta biyu a teburi da Chelsea ta hudu da kuma Tottenham ta bakwai.

Bayan da ta buga wasa 33, Leicester wadda Brendan Rodgers ke jan ragama ta kasance a mataki na uku a irin wannan matakin a kan teburi a kakar 2019-20

Source: BBC