Rahotanni daga Isra'ila na cewa gomman mutane sun rasa ransu wasu kuma da dama sun ji raunuka a wani turmutsutsu wurin wani bikin Yahudawa.
Dubban masu ibada ne suka taru a kasan tsaunin Meron da ke arewacin kasar domin wannan biki. An ga hotunan tarin gawarwaki da aka sanya a ledoji jere a kasa a wurin da turmutsutsun ya auku.
Al'amarin ya kasance ba kyawun gani yadda ake ganin hotunan bidiyo yadda wurin yake a yamutse ma'aikatan agaji na ta fama kan yadda za su dauke wadanda aka tattake suka ji rauni a turmutsutsun.
Wasu rahotannin farko-farko sun bayyana cewa wani wuri ne da dimbin mutane ke tsaye a kai ya karye, abin da ya kai ga turmutsutsun aka yi ta tattake mutane.
Firaministan Isra'ilar Benjamin Netanyahu ya bayyana lamarin a matsayin babban bala'i, kuma an tura sojojin kasar domin su taimaka da agaji.
'Yan uwa da iyalai cikin fargaba na ta kokarin kiran wayar nasu da ke wurin domin sanin halin da suke ciki, amma kuma wasu rahotanni na cewa layukan wayar ma ba sa kamu, saboda an samu matsala ta katsewa.
Wannan dai shi ne wani taro mafi girma a kasar ta Isra'ila tun barkewar annobar korona, kuma daman an yi ta suka kan yin taron saboda hadarin yada cutar.
A bara an hana taron ibadar saboda gudun baza kwayar cutar ta korona.To amma a bana aka sassauta matakan yaki da korona saboda nasarar da aka samu a riga-kafin annobar a kasar ta Israi'la wanda yana daya daga cikin mafiya sauri a duniya
Sai dai wani dan jarida da yake wurin ya ce babu wani abin tsayuwa da ya karye turmutsutsu ne kawai;
Ya ce, : ''Mutane ne sama da dubu daya suka yi kokarin wucewa ta dan wani tsukin titi, sai kawai suka rika faduwa a kan junansu.Babu wani abu da ya karye, sun fadi ne a kan juna kawai, zuwa yanzu dai ma iya cewa akwai kusan mutane biyar da suka mutu, tabbas arba'in, amma suna tunanin kusan hamsin. Sama da mutane dari daya sun ji munanan raunuka.''
Tun da farko dama jami'ai sun ce sun kasa sanya mahalatta taron ibadar bin dokokin kariya na korona saboda yawa. 'Yan sanda sun ce sun kama mutum biyu da suka kawo musu cikas wajen tabbatar da bin doka, kafin turmutsutsun ya barke.
Dubban Yahudawa mabiya addinin gargajiya ne ke zuwa wanan taron ibada a kowa ce shekara, inda suke shafe dare suna kunnan wuta da adu'o'I suna kuma rawa.
Wurin taron nasu na daya daga cikin wurare mafiya tsarki a wurin Yahudawan duniya.
Jaridar Times ta Isra'ila ta ce masu shirya taron sun kiyasta masu iabada kusan dubu dari daya ne za su hallara tun a daren da ya gabata na Alhamis, kuma karin wasu za su isa wurin a yau Juma'a.