Menu

Jihar Kaduna: An sa zare tsakanin iyayen dalibai da Gwamna El-Rufai

 118164368 Mediaitem118164367 Nasir El-rufa'i, Gwamnan jihar Kaduna

Fri, 23 Apr 2021 Source: BBC

Wata sabuwar dambarwa ta barke tsakanin iyayen dalibai a jihar Kaduna da kuma gwamnatin jihar karkaashin jagorancin Gwamna Nasir El-rufa'i, dangane da ƙarin kuɗin makaranta da a cewarsu ya wuce hankali.

An yi ta yaɗa takardu a shafukan intanet da ke nuna sabon jadawalin ƙarin kuɗin makarantu ciki har da na Jami'ar Jihar Kaduna, wanda ya janyo fargaba a tsakanin iyayen dalibai.

Mahukunta dai sun ce ko da yake takardun da ake yadawa ba sa kunshe da bayanan gaskiya, amma dai gwamnati na shirin yin ƙarin kudin makaranta ga dalibai a jihar.

Gwamnatin ta ce tabbas za ta yi ƙarin kuɗin makaranta, a ƙoƙarinta na inganta ilmi da kuma daidaita tsarin da halin da ake ciki.

Akasarin daliban da BBC ta zanta da su sun bayyana cewa karin kudin makarantar ya zo musu da bazata, kasancewar dama ana kukan targade sai ga karaya ta samu.

Cikin bayanan da aka rika yadawa dai an ga karin ninkin-ba-ninkin na kudin makaranta, a wani bangaren kuma an ninka kudin makarantar har kusan sau dubu, lamarin da ya sa dalibai suka shiga halin fargaba.

Suma hukumomin jami'ar jihar Kaduna sun ce tabbas akwai maganar karin kudin makarantar, amma ba a kai ga amincewa da adadin yawan karin ba tukuna.

Shugaban jami'ar jihar Kaduna, Farfesa Muhammad Tanko, ya bayyana wa BBC Hausa cewa yamadidin da ake yi cewa an kara kudin makaranta fiye da kima ba gaskiya ba ne.

Haka kuma Farfesa Tanko ya ce tuni gwamnatin jihar Kaduna ta ware Naira Biliyan biyu don tallafa wa dalibai ta yadda iyaye ba za su sha wahalar biyan kudin makaranta ba idan aka amince da sabon karin.

Wata majiya daga gwamnatin Kaduna ta shaida wa BBC cewa karin zai shafi har makarantun firamare da na sakandire, ko da yake shi ma ba a kai ga cimma matsaya ba tukuna.

Source: BBC