An kwantar da babban dantakara na hamayya na Dumokuradiyyar Kongo Guy-Brice Parfait Kolelas, bayan da ya kamu da cutar Korona, lamarin da ya sa ake tababa kan gudanar da zaben shugaban kasar da aka shirya yi Lahadin nan.
Tsarin mulkin kasar ya bayar da damar jinkirta zabe idan wani dan takara ya mutu ko kuma ba zai iya shiga zaben ba saboda wata larura.
Mr Kolelas, wanda ya kasance daya daga cikin 'yan takara bakwai a zaben kasar ta Dumokuradiyyar Kongo, shi ne fitacce kuma jigo a bangaren 'yan hamayya da ke kalubalantar Shugaba Denis Sassou Nguessou, wanda ke kan mulki tsawon shekara talatin da bakwai kuma da dama na ganin shi ne dai zai sake cin zaben.
Shugaban kwammitin yakin neman zaben dan takarar na hamayya ya tabbatar da sahihancin wani hoton bidiyo da ake yadawa a shafukan intanet da ke nuna Mista Kolelas mai shekara sittin da daya, kwance a galabaice a gadon asibiti.
A hoton bidiyon ana ganin Mista Kolelas sanye da na'urar taimaka masa da iskar shaka, wadda ya dan cire na dan lokaci a da kyar da kyar yana gaya wa magoya bayansa cewa yana cikin mawuyacin hali na sai yadda ta kasance.
Sai dai duk da haka ya bukaci magoya bayan nasa da su fita su yi zaben domin domin tabbatar da canji.
Shekaran jiya Juma'a ne aka gano cewa babban dan takarar na hamayya, na Jamhuriyar ta Kongo, Mista Kolelas, wanda daman yana da cutar sukari, ya kamu da cutar korona.
Iyalansa sun ce suna kokarin ganin yadda za a dauke shi daga asibitin da yake na 'yan kasuwa a babban birnin kasar, Brazzaville, zuwa Faransa domin yi masa magani.
Mista Kolelas ne ya zo na biyu, da kusan kashi goma sha biyar cikin dari na kuri'un da aka kada, bayan Sassou N'Guesso a zaben shugaban kasar na 2016.
A kwanakin nan dan hamayyar ya rika caccaka da sukar shugaba mai ci, har yana cewa Jamhuriyar Kongo ta zama kasa ta mulkin kama-karya da danniya.
Denis Sassou N'Guesso ya kasance shugaba na uku a nahiyar Afirka da ya dade a kan mulki, inda ya kama mulkin kasar daga 1979 zuwa 1992, sannan kuma ya kara kama iko tun daga 1997 har zuwa yau a kasar da katafariyar makwabciyarta Jamhuriyar Dumokuradiyyar Kongo ta sa ba a jin duriyarta sosai.