Menu

Kaciyar mata: Wasu mata sun bayyana tashin hankalin da suka shiga bayan yi musu

 117803636 D4405047 Ebd2 4708 8ca2 1d7201cb464d Mata sun dade suna bayyana tashin hankalin da suke shiga bayan kaciya

Sat, 10 Apr 2021 Source: BBC

"Sun bankare ni a kasa suka yanke wannan bangare na jikina - ba ni da masaniyar mene ne dalili. Wannan ita ce azaba ta farko da na taba fuskata a rayuwata.

"Ban san laifin da na aikata ga wadannan tsofaffi ba - na rashin ƙauna - har da za su banƙare ni da karfi su bude kafafuna su ji min rauni. Ya kasance kamar tabuwar kwakwalwa a gare ni.''

Layla (ba sunanta na gaskiya ba) lokacin shekarunta 12 lokacin da aka yi mata kaciyar matan.

A tsakanin al'umomin Musulmai masu ra'ayin rikau a kasar Masar musamman a yankunan karkara ana daukar mata a matsayin ''wadanda ba su da tsarki'' ba su isa aure ba'' muddin ba a yi musu kaciyar ba.

An haramta wannan al'ada a kasar Masar tun a shekarar 2008 - za a iya yanke wa likitoci hukuncin dauri a gidan kaso har na tsawon shekara bakwai muddin aka same su da aikata laifin yi wa mata kaciyar.

Kana dun wanda ya bukaci a yi zai fuskanci daurin shekara uku a gidan yari.

Duk da haka kasar na da adadi mai yawa na masu aikata wannan al'ada a duniya.

Ana kuma aikata hakan ne da nufin cewa za a yi ''tiyatar fata'' ne, kamar yadda Reda Eldanbouki, wani lauya mai rajin kare hakkin bil adama wanda ke jagorantar wata cibiya mai tsaya wa mata kan abubuwan da suka shafi bin kadi a kotu kyauta.

Cibiyar ta Women's Centre for Guidance and Legal Awareness (WCGLA) mai mazauni a birnin Alkahira ta shigar da ƙararraki 3,000 a madadin mata kuma ta samu galabar 1,800 daga cikinsu da suka hada ba batutuwa shida na yi wa mata kaciya.

Duk da cewa doka ta goyi bayansu, amma kuma samun a yi musu adalci wani abu daban ne kuma. Ko da an kama su, kotuna da 'yan sanda su kan sassauta wa masu aikata laifin, Eldanbouki ya bayyana.

Ya shaida wa BBC cewa cibiyar na fafutika game da wannan al'ada, kuma ta gabatar da mata uku da suka yi bayani game da halin rayuwar da suka shiga, da kuma dalilan da suka sa suke son su kare sauran mata masu tasowa nan gaba.

Labarin Layla: 'Sun danne ni suka min kaciyaBan san abin da na yi wa tsofaffin matan nan ba'

Kusan shekaru 30 da suka wuce, har yanzu Layla ba za ta taba manta wa da wannan mummunar rana ba. Ta samu cin jarrabawar makarantarta.

"A maimakon a yi mini kyauta kan kyakkyawan sakakon jarrabawa da na samu, iyayena sai suka saka mini da samo wata ungozoma, sanye da bakaken kaya, suka kulle ni a cikin daki suka kewaye ni,'' Layla tana tunawa.

Saboda magana game da kaciyar mata haramci ne mai tsanani da ya sa Layla uwa mai shekaru 44 da 'ya'ya hudu, ba ta son ta bayyana inda take da zama a kasar Masar.

Kakarta da sauran makwabtansu mata biyu na cikin matan da suka kewaye ta a wannan ranar (galibi makwabta ke shirya komai tare su samu ungozoma don gudanar da wannan al'ada a kan 'ya'yansu mata a rana guda).

"Kamar kowa, zama a kauye yawanci mu kan yi kiwon kaji a gida. Lokacin da wannan mata ta yanke min wannan bangare na jikina, sai ta jefa wa kajin da suka taru a wurin su cinye,'' ta tuna.

Tun daga wannan ranar Layla ba ta iya cin nama kaza, ko kuma ajiye su a cikin gida.

"Ina karamar yarinya lokacin kuma an fara hutun makaranta - ina so in yi wasa amma na kasa tafiya, sai dai da ƙafafuna a bude,'' Layla ta ce.

Layla ta dau tsawon lokaci kafin ta gane me ya faru da ita, amma bayan ta girma ta yi aure, ta ce ta fahimci abin da ke biyo bayan rashin yin kaciyar.

"Mutanen kauyen na daukar duk macen da ba a yi wa kaciya ba a matsayin mai aikata sabo, kana wacce aka yi wa mace ce tagari.

Mene ne ma'anar hakan? Me ya hada hakan da kuma halayya mai kyau?

Suna bin al'adar da su kansu ba su fahimce ta ba,'' ta ce.

Lokacin da ta haifi diyarta ta farko Layla ba ta amince ita ma ta shiga irin halin da ta shiga ba, amma ba ta iya hana mijinta shirya yadda za a yi ba. Mijinta na son faranta wa danginsa.

Amma a lokacin da ya kamata za a yi wa sauran 'ya'yan Layla kaciyar, an riga a haramta yi a kasar kuma Layla ta gani a lakcar da cibiyar WCGLA ta yi a shafin intanet da kafar talabijin.

Layla ta fara halartar taron lakcar da Eldanbouki ke gudanarwa, kuma ta samu kwarin gwiwa na kare diyarta ta biyu.

Ta san yadda wasu 'ya'ya matan a wurinsu suka yi ta zub da jini suka mutu saboda wannan tsohuwar al'ada.

"Me zai sa in saka diyata cikin wannna hadari? Saboda al'ada irin ta rashin wayewar kai?

"Na dade da sanin cewa ba daidai ba ne, amma ba ni da madogara kan yadda zan iya jan hankulan sauran mutane.

"Kuma ba mijina kadai ba ne na zan ja wa ra'ayi, har da surukaina da dangina. Su ma duk an yi musu, duk suna ganin daidai ne, kuma duka suna tunanin "kai wane ne da za ka iya sauya duniya'' irin halayyata"

Ta bai wa mijinta wa'adi - ka soke batun yi wa 'ya'yana kaciya ko kuma mu rabu.

"Muna da 'ya'ya hudu, don haka ba ya son ya bar gidan,'' ta ce.

"Amma ina tausaya wa babbar ɗiyata, ta yi ta zub da jini ban iya kare ta ba. Ban kasance tare da ita ba lokacin da abin ke faruwa.''

Labarin Sharifa: 'na yi ta zub da jini bayan an min kaciyar, sai aka garzaya da ni asibiti'

Shekarar Sharifa (ba sunanta na asali ba) goma a lokacin da mahaifinta ya yanke shawarar yi mata kaciya.

"Mahaifiyata ba ta son kaciyar, amma mahaifina da ke son faranta wa mahaifiyarsa da kannensa ya nuna musu ya isa da gidansa, ya dauke ni ya kai ni wajen likita ba tare da ya fada mata ba ."

Sharifa ta yi tunanin likitan ya yi mata allurar dauke ciwo ta gargajiya, wanda ba ita ce ainahin abin da ake amfani da shi ba kamar yadda binciken BBC ya gano.

"Ina ta kuka, ban san dalilin da ya sa mahaifina ya min haka ba. An garzaya da ni asibiti saboda jinin da nake zubdawa,'' in ji Sharifa. "Mahaifina ya tsorata, sai ya fada wa mahaifiyata, ya ji tsoro wani abu mara dadi ya same ni."

"Mahaifiyata da ke fama da hawan jini da ciwon zuciya yanke jiki ta yi ta fadi a lokacin da aka fada mata abin da ya same ni.

"Sai aka kai ta asibitin da nake kwance, kuma a nan ta rasu. A yanzu ina zaune hannun kakata ta wajen uwa."

Bayan rasuwar mahaifiyar Sharifa, mahaifinta ya kara aure.

"Ya aiko min kudi, ya dage a kan na koma makaranta na karanci fannin shari'a, saboda halin da na samu kaina a ciki da mahaifiyata."

Tare da ƙawayenta, suka shiga gangamin wayar da kai kan illar yi wa 'ya'ya mata kaciya, wadda da Eldanbouki da tawagarsa ke jagoranta.

"Ina son na ƙware a fadakarwa kan illar yi wa mata kaciya," in ji Sharifa.

Eldanbouki ya ce akwai jan aiki a gabansu.

A shekarar 2013, an daure wani likita a gidan kaso na watanni uku saboda yi wa 'yar shekara 13 kaciya. Eldanbouki ya gana da likitan da mahaifiyar yarinyar.

"Mutane sun amince da likitan. Dala biyu ake biyansa, ya ce yana yi ne domin Allah," in ji Eldanbouki.

"Likitan ya ce ba laifi ba ne. Ya ce akwai wani tsiro a tsakanin kafafunta, don haka ya cire ma ta ba kaciya ya yi wa yarinyar ba."

Lauyan ya ce duk da cewa yarinyar ta rasu, amma mahaifiyarta ta kafe cewa bai aikata kuskure ba.

"Mun je wajen mahaifiyarta muka tambaye ta: 'Idan da 'yarki tana raye, za ki yi mata kaciya?' Sai mahaifiyar ta ce, 'Kwarai, da zarar an yi mata kaciya, sai kuma aurar da ita.'"

Labarin Jamila: 'Na ji tsoron ungozomar bayan an min kaciya - Ina ganin kamar za ta sake yi min'

Shekarar Jamila, (ba sunanta na ainahi ba), 39, an yi mata kaciya tana da shekara tara.

"Lokacin hutun bazara ne, mahaifiyata ta zo da wata tsohuwa, da maƙwabtanmu mata biyu. Ta shirya komai a waje guda, ta bar matan a daki," kamar yadda Jamila ta iya tunawa.

"Zan iya tunawa, sun cire min wando, matan biyu suka bude kafafuna tare da riƙewa. Ungozomarta ta yi amfani da rezar wajen yi min kaciya, shi kenan," in ji ta.

"Mahaifiyata ba ta wajen, saboda tana jin tsoro ba ta son ganin abin da zai faru."

Baya ga matsananciyar azaba, da tabo da dimuwar da kaciyar ta sanya Jamila, ta ce abin da ya faru ya sauya mata rayuwa.

A baya tana da kokari da surutu a makaranta, amma duk waɗannan sun kau tun bayan yi mata kaciyar. Sai kuma ta fara gudun manyan mata.

"Abin damuwar shi ne, ina yawan haduwa da ungozomar nan akan hanyar zuwa makarantar firamare. Bayan faruwar lamarin sai na sauya hanya don ba na son ganin ta. Ina ganin kamar za ta kara yi min."

Har yanzu Jamila na jin ciwo idan mijinta na saduwa da ita.

"Rayuwar mai tsauri ce, jima'i na zame min azaba. Watakil inda ina jin dadi da zan manta abin a ya faru. Amma yanzu komai babu dadi."

Jamila ta ƙudurci ba za ta bari ƴarta ta shiga halin da ta samu kanta a ciki ba. Bayan halartar tarukan wayar da kai, ta shirya wata lakca a gidanta wanda Eldanbouki ya gabatar.

"Ina ganin shi ne babban dalilin da ya sa nake son kaucewa yi wa 'yata. Tare da mijina muke halartar laccar, zuriyarsu sun daina yi wa mata kaciya."

A bangare guda, Eldanbouki ya ce yana fuskantar cin zarafi da wulakanci saboda gangamin da yake yi na yaki da al'adarsu.

"A wani lokaci da muke taron wayar da kai kan illar yi wa mata kaciya, wani mutum ya zo ya tofa min yawu a fuska, ya kuma ce min, "Kana son mayar da 'ya'yanmu mata karuwai a Amurka."

Amma Jamila ta ce ana samun sauyi.

"Na fara ganin adadin wadanda ke yi wa 'ya'yansu mata kaciya ya na raguwa. Na fada wa 'yata da take aji uku na sakandare. Ina ba ta ƙwarin gwiwar yin rubutu akan kaciuyar mata a makaranta."

'Yar Jamila tana zaune a gefenta a lokacin da take hirar da BBC.

Kamar yadda asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya , Unicef, ya sanar kashi 87 cikin 100 na mata 'yan shekara 15 zuwa 49 a kasar Masar an yi musu kaciya, kashi 50 cikin 100 sun yi amanna da cewa ''addini ne ya amince a yi hakan''.

Wannan makala ce da aka rubuta da taimakon Reem Fatthelbab ta sashen Larabci na BBC. Jilla Dastmalchi ce ta rubuta.

Source: BBC