Chelsea ta huce haushi a kan FC Porto, inda ta doke ta 2-0 a wasan farko na daf da na kusa da na karshe a Champions League da suka kara ranar Laraba.
Chelsea ta ci kwallon farko ta hannun Mason Mount daga baya ta ci na biyu daf da za a tashi ta hannun Ben Chilwell.
Ranar Asabar West Brom ta ci Chelsea 5-2 a gasar Premier da hakan ya kawo karshen wasa 14 da Thomas Tuchel ya yi a kungiyar ba tare da an doke shi ba a dukkan fafatawa.
Haka kuma Chelsea ta ci karo da kalubale a ranar Lahadi, bayan da Antonio Rudiger da Kepa Arrizabalaga suka yi rigima sai da aka shiga tsakaninsu a lokacin atisaye.
Porto ta Chelsea sun buga karawar ta Champions League a Sevilla a filin da ake kira Ramon Sanchez Pizjuan a Spaniya.
Hakan ya biyo bayan dokar hana shiga kasa tsakanin Portugal da Burtaniya domin gudun yada cutar korona.
Ranar 13 ga watan Afirilu Chelsea za ta karbi bakuncin FC Porto a wasa na biyu a dai Sevilla a matakin gidan kungiyar Stamford Bridge.