Menu

Kano: An kama mutumin da ke sayar da lemun da ya janyo ɓarkewar baƙuwar cuta

 117588943 Mediaitem117588942 Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje

Tue, 16 Mar 2021 Source: BBC

Hukumar kare hakkin masu sayen kayan masarufi ta jihar Kano tace ta kama wasu mutum huɗu da ake zargin su da sayar da lemonn nan ɗan tsami, da ya haifar da wata baƙuwar cuta da kan sa mutane fitsarin jini da kuma yin amai.

Mukadashin shugaban hukumar Baffa Babba Danagundi ya shaidawa BBC cewar sun kama mutanen ne a wani kango a garin Minjibir.

Ya ce an samu tarin kayan da yawansu ya kai buhu kusan ɗari biyar da tamanin da uku da dukkansu lokacin amfaninsu ya ƙare, ciki har da lemukan ƙarin ɗandano.

Ya ƙara da cewa sun kuma gano cewa ''Shi kansa mutumin dake matsayin jagoransu ashe aikinsa kenan, wasu abubuwan da aka gano a kangon ma idan ka buɗe su bazaka iya tantance ko menene ba''

Baffa Babba ya bayyanawa BBC cewa sun gano mutanen ne bayan zurfafa bincike a wuraren da ake sayarwa mutane lemon da suka haɗar da Bakin Asibiti, da Kasuwar Rimi da ta Singa da kuma Sabon Gari.

Su dai hukumomin lafiya a jihar Kanon sun tabbatar da mutuwar mutum hudu sakamakon wannan cuta.

Shugaban kwamitin kar-ta-kwana na cibiyar dakile cutuka masu yaduwa da ke asibitin Muhammadu Abullahi wasai, Dakta Bashir Lawal ne ya tabbatar wa BBC hakan .

Ya ce tun da farko sun samu labarin bullar wannan cuta wadda mutanen da ta kama ke fitar da jini da amai da gudawa, hakan ya sa suka yi tsammanin cutar lassa ce saboda alamominsu sun yi kama da juna, amma bayan gudanar da bincike an gano ba Lassa ba ce.

Kwararren likitan ya ce "Mutum hudu sun mutu dalilin wannan cuta, ta kashe biyu a asibiti da kuma kashe mutum biyu da suke jinya a gida.

Sannan ya zuwa yanzu cutar ta kama mutum 189 wadanda suke asibitoci mabambanta da aka ware domin yaki da wannan cuta.

Source: BBC