Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta yi nasarar doke Adamawa United da ci 1-0 a wasan mako na 21 da suka kara ranar Lahadi.
Pillars wadda ke buga wasanninta na gida a jihar Kaduna ta zura kwallo a raga ne ta hannun kyaftin, Rabi'u Ali, kuma sauran minti 10 a tashi daga fafatawar.
Da wannan sakamakon Pillars ta ci gaba da zama a mataki na biyu a kan teburi da maki 40 iri daya da na Akwa United wadda take ta daya, bayan da ta ci Dakkada 2-0.
Jumulla wasa tara aka buga a karawa ta 21 a gasar Firimiyar Najeriya ranar Lahadi, wadda aka ci kwallo 13, sannan kungiyoyi hudu suka ci wasa a waje.
Rivers United ta je ta doke Rangers 1-0, Akwa United ta dura biyu a ragar Dakkada, Mountain of Fire ma ta ci 2-0 a gidan Warri Wolves da wanda Nasarawa United ta je ta doke Wikki da ci 2-1.
Wannan shi ne karon farko da kungiyoyin gida har hudu da suka sha kashi tun bayan mako na 15 a bara da aka yi irin wannan bajintar.
Sakamakon wasannin mako na 21 a gasar Firimiyar Najeriya: