Juventus ta je ta doke Cagliari 3-1 a wasan mako na 27 da suka fafata a gasar Serie A ranar Lahadi.
Cristiano Ronaldo ne ya ci wa Juventus kwallo ukun rigis kuma a karon farko a bana, sannan na uku da ya yi wannan bajintar a kungiyar.
Kyaftin din Portugal, mai shekara 36 ya ci kwallon farko da kai, sannan ya ci na biyu da kafar hagu a bugun fenariti ya karkare na uku da kafar dama.
Ronaldo wanda ya koma Juventus a cikin watan Yulin 2018 ya fara cin kwallo uku rigis a Champions League a wasa da Atletico Madrid cikin watan Maris 2020.
A gasar Serie A kuwa, Ronaldo ya ci kwallo uku a karon farko cikin watan Janairun 2020 wasan da Juventus ta doke Cagliari 4-0 ranar 6 ga watan Janairun 2020.
Cagliari ta zare kwallo daya ne ta hannun Giovanni Simeone, kuma kungiyar tana ta 17 a kasan teburi da maki 22.
Wannan ne karon farko da aka yi nasara a kan kocin Cagliari, Leonardo Semplici tun bayan da ya karbi aiki a cikin watan Fabrairu.