Menu

Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Lingard, Edouard, Haaland, Sancho, Boateng, Tomori

 115929241 Gettyimages 1179075965 Jesse Lingard, dan wasan West Ham

Wed, 14 Apr 2021 Source: BBC

Paris St-Germain, Real Madrid da Inter Milan suna sanya ido kan halin da Jesse Lingard' yake ciki kafin bude kasuwar musayar 'yan kwallo ta bazara. Dan wasan na tsakiya mai shekara 28 dan kasar Ingila yana burge West Ham tun da ya je zaman aro a can daga Manchester United. (ESPN)

Arsenal tana ci gaba da nuna sha'awar dan wasan gaban Celtic Odsonne Edouard kodayeke tana fuskantar kalubale daga Leicester a yunkurin daukar dan wasan na Faransa mai shekara 23 da ke buga gasar 'yan kasa da sekara 21. (Telegraph - subscription required)

Manchester United tana ɗari-ɗarin soma tattaunawa da Borussia Dortmund game da daukar dan wasan gaban Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 20, saboda a bazarar da ta wuce Dortmund ta ki rage farashin da United ke son dauka Jadon Sancho. (The Athletic - subscription required)

Duk da rashin samun nasara a waccan tattaunawar, har yanzu Manchester United ba ta fitar da rai wajen daukar dan wasan gaban Ingila Sancho, mai shekara 21, a bazarar nan ba. (Manchester Evening News)

Manchester United ta dawo da sha'awarta ta son daukar dan wasan tsakiyar Lazio Sergej Milinkovic-Savic. Real Madrid da PSG su ma suna son dan wasan dan kasar Serbia mai shekara 26. (Gazzetta - in Italian)

Tottenham na shirin mika bukatarta ta daukar dan wasan bayan Bayern Munich Jerome Boateng, mai shekara 32. Dan wasan na Jamus zai bar Munich a karshen kakar wasa ta bana. (Sky Germany - in German)

Tottenham za ta mayar da hankali wajen inganta tsaron bayanta a bazarar nan ama dole ta soma sayar da wasu 'yan wasa domin ta samu kudin cimma burinta. (Mail)

AC Milan ta sha alwashin sayen dan wasan Ingila mai shekara 23 Fikayo Tomori a mataki na dindindin - wanda ya ke zaman aro daga Chelsea. (Corriere dello Sport, via Sport Witness)

Eddie Howe, Frank Lampard da kocin Burnley Sean Dyche na cikin jerin mutanen da Crystal Palace take neman dauka domin maye gurbin Roy Hodgson a matsayin koci. Kwangilar Hodgson za ta kare a karshen kakar wasan bana. (Football Insider)

Bayern Munich na son daukar dan wasan baya na Sifaniya Lucas Vazquez, wanda watakila ba zai sake buga wasa a Real Madrid ba. Watakila raunin da dan wasan mai shekara 29 ya ji a gwiwarsa ba zai ba shi damar sake buga tamaula a har zuwa karshen kakar wasan bana, lokacin da kwangilarsa za ta kare. (Marca)

Juventus na matukar son daukar dan wasan Barcelona da Faransa Ousmane Dembele, mai shekara 23, idan kwangilarsa ta kare a 2022. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Source: BBC