Chelsea na duba yiwuwar daukar dan wasan Belgium kuma tsohon dan wasanta Romelu Lukaku, mai shekara 27, idan ta gaza daukar dan wasan Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 20, a bazarar nan. (Telegraph)
Manchester City tana son daukar Lukaku, wanda ya zura kwallo 59 a wasanni 85 da ya murza a Inter Milan. (Calciomercato, via Manchester Evening News)
Borussia Dortmund ta sanya kudi kan Haaland ga masu son daukarsa a bazarar nan inda ta ce duk kungiyar da ke son dan wasan za ta ajiye akalla £154m. (ESPN)
Dan wasan Senegal Sadio Mane, mai shekara 28, ya bayyana cewa zai ci gaba da zama a Liverpool - koda kuwa kungiyar da Jurgen Klopp yake jagoranta ba ta samu gurbin zuwa gasar Zakarun Turai na kakar wasa mai zuwa ba. (Sun)
Kofar Manchester United a bude take ga dan wasan Ingila mai shekara 28 Jesse Lingard, wanda ke zaman aro a West Ham - kuma akwai damar sake tattaunawa domin tsawaita kwangilarsa. (Sun)
Manchester United ta tuntubi Atletico Madrid domin daukar dan wasan Sifaniya Marcos Llorente, mai shekara 26, a kan £68.5m. (AS)
Rahotanni sun ce ran shugaban Real Madrid Florentino Perez 'ya yi matukar baci' game da Manchester United saboda ta bi sawunta a yunkurin daukar dan wasan Sifaniya mai shekara 24 Pau Torres. (El Desmarque, via Mirror)
Kocin Liverpool Klopp ya sake bukatar masu kungiyar su amince a sabunta kwangilardan wasan tsakiya na kasar Netherlands Georginio Wijnaldum, mai shekara 30. (90min)
Kazalika Liverpool na gaban AC Milan da Juventus a yunkurin daukar dan wasan PSV dan kasar Netherlands Donyell Malen, mai shekara 22, a bazarar nan. (Gazetta dello Sport, via Mail)
AC Milan za ta "yi dukkan mai yiwuwa" domin daukar dan wasan Ingila mai shekara 23 Fikayo Tomori a mataki na dindindin daga Chelsea, a cewar mataimakin shugaban kungiyar Franco Baresi. (Gazzetta dello Sport, via Standard)
Dan wasan Newcastle United dan kasar Paraguay Miguel Almiron, mai shekara 27, ya ce yana 'son murza leda a kungiyoyin da ke fafatawa sosai' yayin da ake rade radi game da makomarsa a Tyneside. (Chronicle)