Dan wasan gaban Brazil Neymar, mai shekara 29, ya amince ya tsawaita zamansa a Paris St-Germain zuwa 2026 - don haka yanzu kungiyar ta Faransa ta mayar da hankali wajen sabunta kwangilar Kylian Mbappe, mai shekara 22. (Telefoot, via AS)
Kudin sayen dan wasan Borussia Dortmund Erling Braut Haaland zai iya karuwa da euro 40m (£34m), saboda wakilinsa Mino Raiola da mahaifinsa Alf-Inge suna so a bai wa kowannensu euro 20m (£17m) a matsayin kudin la'ada a wani bangare na yarjejeniyar sayar da shi. (RAC1, via Marca)
Kazalika akwai kudin darajar dan wasan da ke kan Haaland wanda ya kai euro 75m (£64m) da za a titalas wa kungiyar da za ta saye shi ta biya idan ya kai shekra mai zuwa amma zai iya barin Dortmund a bazarar nan a yayin da kungiyar ta kasa katabus a Bundesliga ko kuma idan ta kasa samn gurbin gasar Zakarun Turai. (Sun)
Ana alakanta dan wasan Norway Haaland, mai shekara 20 da son tafiya Barcelona sai dai koci Ronald Koeman ya ce shugaban kungiyar Joan Laporta ne kawai zai yanke hukunci kan daukar dan wasan. (AS)
Lionel Messi yana jira ya ga tsarin da Laporta ya yi game da makomar Barcelona kafin ya yanke shawara a kan ko ya ci gaba da murza leda a kungiyar ko kuma ya tafi PSG ko Manchester City. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Angel di Maria ya ce yana so ya murza leda tare da dan kasarsa ta Argentina Messi a PSG idan dan wasan mai sekara 33 ya bar Barcelona. (beIN Sports, via Goal)
Kocin Leicester Brendan Rodgers yana fatan sayen dan wasan tsakiyar Scotland Callum McGregor, mai shekara 27, daga tsohuwar kungiyarsa Celtic. (Sun)
Kocin West Ham David Moyes ya ce a bazarar nan kungiyar za ta amince da tayin da kungiyoyi suke yi na daukar dan wasan Ingila Declan Rice, mai shekara 22, da takwaransa na Jamhuriyar Czech Tomas Soucek, mai shekara 26. (Mirror)
Manchester United da Juventus suna nuna sha'awar sayen dan wasan Barcelona da Faransa Ousmane Dembele, mai shekara 23, amma har yanzu Liverpool da PSG suna son dan wasan. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Kocin Chelsea Thomas Tuchel ya tura dan wasan Jamus Antonio Rudiger, mai shekara 28, domin ya yi atisaye da wurwuri ranar Lahadi bayan ya yi musayar yawu da golan Sifaniya Kepa Arrizabalaga, mai shekara 26, sakamakon kashin da suka sha da ci 5-2 a hannun West Brom ranar Asabar. (Telegraph - subscription required)
Dan wasan Everton da Colombia Yerry Mina, mai shekara 26, yana son tafiya Serie A a bazarar nan, inda Inter Milan da Fiorentina suke son dan wasan. (Sun)
Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya ce ba za su dauko dan wasan Argentina Sergio Aguero, mai shekara 32, daga abokan hamayyarus Manchester City ba idan kwangilarsa ta kare a karshen kakar wasan bana. (Goal)