Menu

Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Origi, Gibbs, Van de Beek, Elneny, Dybala

 117615550 Mediaitem117615549 Dan wasan Liverpool da Belgium Divock Origi

Thu, 18 Mar 2021 Source: BBC

Borussia Dortmund na son daukar dan wasan Liverpool da Belgium Divock Origi, 25, kuma tana iya neman daukarsa a bazara. Origi, wanda ya zura kwallo a wasan karshe na gasar Zakarun Turai a kakar wasan bara waccan, za a iya sayar da shi a kan £12m. (Football Insider)

Tsohon dan wasan Arsenal da Ingila Kieran Gibbs, mai shekara 31, ya amince ya tafi Inter Miami a karshen kakar wasan da muke ciki inda ya yarda da yarjejeniyar shekara biyu da rabi da zarar kwangilarsa ta kare a West Brom. (ESPN)

Dan wasan tsakiyar Netherlands Donny van de Beek, mai shekara 23, ya ce ya ji dadin "kaunar" da aka nuna masa a Manchester United amma yana so ya soma buga wasanni da dama, a cewar kocin Netherlands Ronald de Boer. (Talksport)

Joan Laporta - mutumin da ya soma wa'adi na biyu na shugabancin Barcelona - ya ce zai yi kokari ya rarrashin dan wasan Argentina Lionel Messi ya ci gaba da zama a kungiyar. Dan wasan, mai shekara 33, wanda zai sake kafa sabon tarihi a Barcelona idan ya buga wasan da za su yi na gaba, kwangilarsa za ta kare a karshen kakar wasan bana. (Goal)

Dan wasan Arsenal da Masar Mohamed Elneny, mai shekara 28, yana son ya sanya hannu kan sabon kwantaragi kuma ya ce bai yi tunanin cewa zamansa ya kare a Gunners ba lokacin da ya tafi zaman aro a Besiktas a kakar wasan da ta wuce. (Evening Standard)

Dan wasan Chelsea da Jamus Antonio Rudiger, mai shekara 28, ya bayyana cewa Paris St-Germain da Tottenham sun so karbar aronsa a kakar wasan da ta gabata. (Times, subscription required)

Juventus ta shirya sayar da dan wasan Argentina Paulo Dybala inda aka bai wa Tottenham da Chelsea daukar dan wasan mai shekara 27. (Star)

Dan wasan West Ham Michail Antonio, mai shekara 30, ya ce makomarsa kan wasannin kasashen duniya tana hannun Jamaica, ba Ingila ba. (Sky Sports)

Source: BBC