Menu

Kasuwar 'yan bal: Haaland, Sancho, Messi, Salah, Ibrahimovic, Foyth

 117852112 Adb191f6 0181 4184 A953 Be18426151c0 Dan wasan Barcelona, Lionel Messi

Tue, 6 Apr 2021 Source: BBC

Babban dillalin 'yan wasa Mino Raiola ya mayar da kakkausan martini kan rade-radin da ake yi game da sayar da dan wasan gaba na Borussia Dortmund, dan kasar Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 20, kamar yadda Goal ta ruwaito.

Shugaban Borussia Dortmund Hans-Joachim Watzke ya kara jaddada cewa suna tsare-tsaren kaka ta gaba tare da Haaland, a ruwayar Dazn daga jaridar Mirror.

Sai dai kuma ya ce kungiyar ta Jamus za ta saurari bukatar sayen dan wasan ta na gefe Jadon Sancho, dan Ingila, in ji jaridar Manchester Evening News.

Mai horas da 'yan wasan Manchester United Pep Guardiola ya ce jagorar Premier ka iya kashe sama da fam miliyan dari daya wajen sayen dan wasa daya kacal a nan gaba, amma ya yi gum da bakinsa game da rade-radin da ake yi cewa kungiyar za ta sayi Haaland, kamar yadda labarin ya bayyana a Sky Sports.

Ita kuwa kungiyar Barcelona za ta ci gaba da kokarin ganin ta sayi matashin dan wasan dan Norway bayan da ta gana da wakilansa a makon da ya gabata, to amma kuma wasu majiyoyi daga kungiyar sun ce abu ne mai wuya cinikin ya yiwu. Ruwayar ESPN

Kociyan Real Madrid Zinedine Zidane ya kawo karshen shirun da yake yi game da rade-radin cewa kungiyar za ta sayi dan wasan gaba na Liverpool kuma dan Masar Mohamed Salah, mai shekara 28, in ji jaridar Liverpool Echo.

Tsohon janar manajan Real Madrid Jorge Valdano, na da ra'ayin cewa abu ne da zai dace kungiyar ta Los Blancos ta yi amfani da dan wasan Brazil na gefe, Vinicius Junior, mai shekara 20, a matsayin wani bangare na shirinta na sayen dan wasan Paris St-Germain kuma dan gaba na Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 22, kamar yadda El Transistor ta ruwaito daga Marca

Dana wasan gaba na Paris St-Germain da kuma PSG Angel di Maria, mai shekara 33, ya ce abu ne da zai yi matukar kauna ya taka leda a kungiya daya da Lionel Messi, mai shekara 33, yayin da ake rade-radi kan shakkun kasancewarsa a Barcelona nan gaba, kamar yadda AS ta ruwaito

Tsohon dan wasan gaba Zlatan Ibrahimovic, mai shekara 39, na shirin kara tsawon yarjejeniyar zamansa a AC Milan da shekara daya, in ji Sky Sports

Ana nazari da duba dukkanin tawagar 'yan wasa da kuma jami'an kungiyar Juventus a tsawon sauran lokacin da ya rage na wannan kaka sakamakon rashin tabuka abin-a-zo-a-gani da kungiyar ta yi a bana, wanda ke iya sa zakarun na gasar Italiya su kasa samun damar gasar Zakarun Turai, in ji jaridar Mail.

Source: BBC