Manchester United da Arsenal na daga cikin kungiyoyin da ke sa ido kan dan wasan gaba na kungiyar Borussia Monchengladbach Alassane Plea, mai shekara 28, dan kasar Faransa. (Jaridar Mail)
Manchester United za ta saka wa dan wasanta na baya na gefe dan Ingila Luke Shaw, mai shekara 25, da sabon kwantiragin zama a kungiyar saboda kwazonsa a wannan kakar. (Jaridar Star)
Dan wasan gaba na Manchester United din kuma dan Uruguay Edinson Cavani ya tattauna da kociyansu Ole Gunnar Solskjaer a kan tsawaita zamansa a kungiyar da karin shekara daya, amma kuma Cavani mai shekara 34 ya nuna cewa shi dai ya fi son tafiya kusa da iyalansa, Latin Amurka, inda ake ganin zai je Boca Juniors. (Jaridar Mirror)
Inter Milan na nan daram wajen zawarcin dan wasan gaba na Manchester City, dan Argentina Sergio Aguero, amma kuma har yanzu ana ganin Barcelona ce a karshe za ta yi nasarar janye Agueron mai shekara 32. (Jaridar Tuttosport daga Sun)
Barcelona ta sanya farashin fam miliyan 44 a kan dan wasanta na gaba kuma dan Faransa Ousmane Dembele, mai shekara 23, wanda rahotnni ke cewa Manchester United da Liverpool na zawarcinsa. (Jaridar Sport)
Ajax ta ce a shirye take ta sayar da dan bayanta na gefen hagu, dan kasar Argentina Nicolas Tagliafico, mai shekara 28, a kan fam miliyan 13,wanda kungiyoyin Leeds United da Manchester City da kuma Inter Milan dukkaninsu ke sha'awa. (Mail).
Manchester United na harin mai tsaron ragar Aston Villa, dn Ingila Tom Heaton, mai shekara 35, idan Sam Johnstone, mai shekara 28, shi ma dan Ingila na kungiyar West Brom, ya nun aba ya son komawa kungiyar. (Jaridar Sun)
Darektan wasanni na Paris St-Germain Leonardo ya ce kungiyar ta Faransa ba za ta yi gaggawar kulla sabuwar yarjejeniya ba ta zaman dan wasanta na gaba dan kasar Brazil Neymar, mai shekara 29. (Jaridar Goal)
Chelsea na son sayen dan wasan gaba a wannan bazara inda ta fi mayar da hankali a kan tauraron dan wasan Borussia Dortmund, dan kasar Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 20, ko kuma Romelu Lukaku, na Inter Milan, dan kasar Belgium mai shekara 27. (Jaridar Sun).
Dan bayan Villarreal dan kasar Faransa Pau Torres, mai shekara 24, ya shiga neman shawara daga abokanansa kan shirin tafiyarsa Manchester United. (Jaridar Manchester Evening News).
Arsenal da West Ham United na duba yuwuwar sayen dan bayan Lyon, dan kasar Denmark Joachim Andersen, mai shekara 24, wanda ke zaman aro a Fulham, a bazaran nan. (Jaridar Mirror)
Dan wasan gaba na Italiya Moise Kean, mai shekara 21,wanda ke zaman aro a Paris St-Germain daga Everton, ya ce bai kawar da yuwuwar sake komawa tsohuwar kungiyarsa ba Juventus a nan gaba. (Jaridar Goal)
Watakila Arsenal ta sake komawa kan aniyarta ta neman sayen dan wasan tsakiya na Borussia Dortmund da Jamus Julian Brandt, mai shekara 24, saboda Gunners din na ganin sayen Martin Odegaard, dan Norway, wanda yake zaman aro a kungiyar ya zama nata dindindin, daga Real Madrid zai yi mata tsada da yawa. (Jaridar Bild daga Express)
Manchester City ba za ta tura dan wasan gaba Kayky aro zuwa wata kungiya a yanzu ba, bayan da ta sayi dan Brazil din mai shekara 17 daga Fluminense. Kungiyar ta Premier na ganin matashin dan wasan zai yi saurin samun damar shiga cikin tawagar gwanayen 'yan wasanta. (Jaridar Athletic)
Dan bayan kungiyar Metz da kasar Mali Boubakar Kouyate, mai shekara 24, na dukar hankalin kungiyoyi da dama da suka hada da Roma da Atalanta, da Southampton da Norwich City da kuma Newcastle United, wadd ita kuma har da abokin wasansa Metz din Pape Matar Sarr take son s\ye. Pape dan wasn tsakiya mai shekara 18 dan kasar Senegal, wasu rahotanni na cewa Chelsea da Everton ma na sha'awarsa. (Jaridar L'Equipe)
Juventus na fatan janye mai tsaron ragar AC Milan Gianluigi Donnarumma, mai shekara 22, ta hanyar ba shi albashi mai tsoka fiye da wanda yake samu a yanzu. Kwantiragin golan na Italiya zai kare a San Siro a bazaran nan kuma har zuwa yanzu bai amince da kulla wata sabuwar yarjejeniya ba. (Jaridar Corriere dello Sport)
AC Milan ta tsara mai tsaron gidan Lille da Faransa Mike Maignan mai shekara 25 zai maye gurbin golanta Donnarumma . (Jaridar Calciomercato)
Tottenham na sa ido a kan matashin dan wasan gaba na Northampton Town dan Ingila asalin Najeriya Caleb Chukwuemeka mai shekara 19. (Jaridar Football Insider)