Menu

Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Lampard, Flick, Haaland, Sancho, Romero, Parker, Berge

 118486175 Franklampard Tsohon kocin Chelsea Frank Lampard

Fri, 14 May 2021 Source: BBC

Tsohon manajan Chelsea Frank Lampard ya na sahun gaba wajen maye gurbin Roy Hodgson a Crystal Palace. Kwantiragin tsohon kocin Ingilan Hodgson zai kare a kakar wasan bana.(Telegraph)

Barcelona na tuntubar wakilan kocin Bayern Munich Hansi Flic, sakamakon tababatar da ake yi kan makomar manajan su na yanzu Ronald Koeman. (ESPN)

Mai kungiyarBorussia Dortmund Hans-Joachim Watzke ya ce dan wasan gaba na Norway Erling Braut Haaland mai shekara 20, zai ci gaba da kasancewa a kulub din har zuwa kakar wasa ta gaba. (ESPN, via Bild)

Wanda ake sa ran zai horas da 'yan wasan Bayern Munich nan gaba Oliver Kahn ya ce bai zaci za a dauke dan wasa Haaland kan farashin fam miliyan 85 ba. (Goal, via Bild)

San wasan Dortmund da Ingila, winger Jadon Sancho, mai shekara 21,na matsawa eja din sa lambar son komawa Manchester United bayan gaza hakan a kakar wasan bara. (Manchester Evening News)

Manchester United ta nuna sha'awar dan wasan tsakiya na Argentine Cristian Romero, mai shekara 23, wanda ya marawa dan wasa Sven Botman mai shekara 21 baya, kuma mai tsaron ragar Dutch da dan wasan Faransa Sevilla mai shekara 22 bayan an fitar da sunayensu na gasar Premier League. (Sky Sports)

Tottenham ta shirya domin fara yin tattaunawa domin cike gurbin manajan ta a kwanaki masu zuwa. Tuni aka bada sunan dan wasan Fulham Scott Parker, sai dai da alama kulub din na fatan dan wasan Leicester CityBrendan Rodgers zai maye gurbin. (Football Insider)

Dan wasan gaba na Senegal Slavia Prague masi shekara 19, da dan wasa Abdallah Sima, na tunanin komawa kungiyar Arsenal da West Ham.(Standard)

Tsohon manajan Bournemouth Eddie Howe ya amince ya zama sabon kocin kungiyar kwallon kafa ta Celtic. (TalkSport)

Ana ta yin daukar dan wasan tsakiya na Faransa Eduardo Camavinga, mai shekara 18, daga kungiyoyi daban-daban, kamar yadda ejan din shi Jonathan Barnett, wanda kuma ya ke wakiltar dan wasaGareth Bale ya bayyana. (Goal)

Source: BBC