Manchester United na ci gaba da sha'awar daukar golan Atletico Madrid Jan Oblak, mai shekara 28, kuma dan wasan na Slovenia zai samu damar sauya kungiya. (90min)
A gefe daya, kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya ce har yanzu dan wasan Uruguay Edinson Cavani, mai shekara 34, ba shi da tabbacin ci gaba da zama a kungiyar a kakar wasa mai zuwa. (Manchester Evening News)
Liverpool za ta iya sayen dan wasan RB Leipzig da ke buga gasar 'yan kasa da shekara 21 a Faransa Ibrahima Konate, mai shekara 21, a kan kasa da euro 40m kamar yadda aka sanar a farkon shekarar nan. (Bild journalist Christian Falk)
Southampton za ta "yi dukkan mai yiwuwa" domin rike dan wasan Denmark Jannik Vestergaard, mai shekara 28, a cewar kocin kungiyar Ralph Hasenhuttl a yayin da wasu rahotanni ke cewa Tottenham na zawarcinsa. (Daily Echo)
Galatasaray ta bai wa dan wasan Crystal Palace Patrick van Aanholt, mai shekara 30, kwangilar shekara uku. Kwangilar dan wasan na Netherlands za ta kare a Palace a karshen kakar wasa ta bana. (Sky Sports)
Liverpool ta shirya mika bukatarta ta sayen Ozan Kabak bayan dan wasan na Turkiyya mai shekara 21 ya burge ta tun bayan da ta karbo aronsa daga Schalke. (90min)
Dan wasan gaban Argentina Mauro Icardi, mai shekara 28, yana neman hanyar barin Paris St-Germain a bazarar nan. (L'Equipe - in French)
Tottenham na kan gaba a cikin kungiyoyin da ke son daukar golan West Brom dan kasar Ingila Sam Johnstone, mai shekara 28. (ESPN)
Crystal Palace want Eddie Howe to replace manager Roy Hodgson after the former Bournemouth boss changed his mind on joining Celtic. (Football Insider)
Southampton na bibiyar dan wasan Tottenham da Ingila Harry Winks, mai shekara 25. (Football Insider)
Dan wasan Arsenal dan kasar Ingila Folarin Balogun, mai shekara 19, yana dab da sanya hannu kan kwangilar shekara hudu a kungiyar. (Guardian)