Menu

Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Sancho, Solskjaer, Allegri, Pochettino, Conte, Donnarumma, Xhaxa

 118701368 Gettyimages 1232991493 Harry Kane, dan kwallon Tottenham da kuma tawagar Ingila

Fri, 28 May 2021 Source: BBC

Kocin Manchester United Solskjaer ya shirya tsaf domin rattaba hannu kan sabon kwantiragin shekara uku a Old Trafford, duk da shan kayen da United ta yi wa Villareal a wasan karshe na Europa League. (Telegraph - subscription required)

Juventus za ta kori mai horas da 'yan wasa Andrea Pirlo tare da maye gurbinsa da tsohon mai shugaban kungiyar Massimiliano Allegri. (Guardian)

Ta yiwu Allegri ka iiya rattaba hannu da kungiyar Juventusnan da sa'a 24. (Sky Sports)

An yi tunanin Allegri zai zamo zabin Real Madrid domin maye gurbin Zinedine Zidane, wanda ya bar kungiyar a ranar Alhamis. A yanzu ana ganin dan wasan Sifaniyar na harin manajan Paris St-Germain Mauricio Pochettino. (Goal)

Tsohon manajan kungiyar Chelsea Antonio Conte, wanda ya bar AC Milan ranar Laraba ya fara nuna sha'awar fara aiki da kungiyar, Tottenham. (Guardian)

Spurs na duba yiwuwar kauda Conte, amma ta fara sanya ido akan Zidane. (Telegraph)

Ana sa ran za a nada Simone Inzaghi a matsayin sabon manajan Inter bayan ya bar Lazio. (Athletic - subscription required)

Za a nada tsohon shugaban kungiyar Sheffield United Chris Wilder a matsayin sabon manajan West Brom. (Mirror)

Tafiyar Conte daga Inter ka iya taimakon dan wasan Arsenal dan Morocco Achraf Hakimi mai shekara 22, ya rattaba kan yarejeniya a Siri-A. (Express)

Chelsea da Tottenham na sha'awar daukar dan wasan tsakiya na kungiyar Borussia Monchengladbach kuma dan Jamus Jonas Hofmann, mai shekara 28. (Kicker - in German)

Source: BBC