Manchester City ta shirya tsaf domin sayar da Raheem Sterling, dan wasan gaba na Ingila mai shekara 26 bayan ya shafe shekara shida a kungiyar. (Mail)
Ɗan wasan gaba na Borussia Dortmund Erling Braut Haaland mai shekara 20 na son ci gaba da zama a kungiyarsa, wanda ke nufin ba inda zai koma ke nan a bana. (Viaplay, via Independent)
Barcelona na da tabbacin dauko Sergio Aguero dan wasan mai shekara 32 daga Manchester City da dan wasan tsakiya na Liverpool kuma dan kasar Holland Georginio Wijnaldum mai shekara 30 dukkansu a kyauta kafin karshen mako mai shigowa. (Sky Sports)
Kocin Chelsea Thomas Tuchel ya ce a shirye yake ya ci gaba da jan ragamar kungiyar ta hanyar sanya hannu kan wata sabuwar kwantiragi. yarjejeniyar da ta kawo Tuchel mai shekara 47 zuwa Stamford Bridge za ta kare ne nan da shekara mai zuwa. (Telegraph - subscription required)
Liverpool na iya samun fam miliyan 80 idan ta sayar da 'yan waanta takwas, cikinsu har da Xherdan Shaqiri mai shekara 29, da dan kasar Belgium kuma dan wasan gaba Divock Origi mai shekara 26, da kuma dan wasan gaba na kasar Japan Takumi Minamino mai shekara 26. (Liverpool Echo)
Raphael Varane, dan wasan baya na Real Madrid mai shekara 28 ya kafe cewa hankalinsa na kan wasannin da Faransa za ta yi ne nan gaba da kuma wasannin gasar UEFA. Wannan na zuwa ne yayin da ake batun komawarsa Manchester United. (Mail)
Aston Villa na son sayo Dwight McNeil, dan wasan gefe mai shekara 21 daga Burnley da kuma Emiliano Buendia mai shekara 24 daga Norwich City. (The Athletic - subscription required)
Tsohon dan wasan tsakiya na Chelsea Oscar, dan wasa mai shekara 29 na son komawa Stamford Bridge - shekara hudu bayan da dan kasar Brazil din ya koma kungiyar Shanghai Port ta kasar China. (Goal)